Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

- Kungiyar Kirista ta Nigeria, CAN, ta ce a tuhumi Gwamna Abdulrazaq na jihar Kwara idan rikici ya barke a jihar

- CAN ta yi wannan jawabin ne game da batun saka hijabi a wasu makarantun gwamnati na jihar da ya tada kura

- Kungiyar ta CAN ta yi ikirarin gwamnan Kwara na nuna bangaranci ta yadda ya ce a bude makarantun da ake rikicin duk da cewa ba a warware matsalar ba

Kungiyar Kirista ta Nigeria, CAN, ta bukaci gwamnatin tarayya da Sufeta Janar na Yan sanda su saka baki kan rikicin Hijabi da ake yi a wasu makarantu da ke jihar Kwara, rahoton Daily Trust.

A sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, Sakataren CAN na kasa, Joseph Bade Daramola ya ce kungiyar ta gano cewa gwamnatin jihar Kwara ta bada umurnin bude makarantun da aka rufe ta tare da warware rikicin ba.

Rikicin Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN
Rikicin Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban JAMB Kan Almundahar N900m

Ya ce hakan yasa wasu da ake zargin yan daba ne sun kai hari wasu coci-coci da makarantun mission sunyi barna.

Ya ce an kai wasu kirista da ba-su-ji-ba ba-su-gani-ba hari ba tare da gwamnan jihar ya dauki wani mataki kare su ba.

DUBA WANNAN: An Rasa Rayuka Sakamakon Hatsarin Da Trela Dauke da 'Yan kasuwa 70 Ta Yi a Bauchi

"Gwamnan Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ne ke da laifi idan lamarin ya tabarbare saboda furucin da ya yi game da saka hijabi a makarantu wadda ya sabawa dokar kotu na cewa kada a dauki wani mataki har sai an warware batun ne ya janyo wannan rikicin.

"Ana bukatar wadanda ke shugabanci su zama masu hikima musamman kan batutuwa kamar addini domin kada a janyo yaki. Idan aka yi wani barna a coci ko aka yi wa wani rauni, Gwamnan Kwara ne ke da laifi," In ji Daramola.

"Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda gwamnatin demokradiyya za ta rika watsi da kiraye-kirayen jama'a tamkar an zabi gwamnan ne domin ya kare addininsa"

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164