Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

- Gwamnatin Jihar Kwara ta raba gardama ta ce dalibai musulmi na iya saka hijabi a dukkan makarantun gwamnati da ke jihar

- Gwamnatin ta ce kotu ta yi watsi da ikirarin da wasu ke yi na cewa makarantun na addini ne saboda sunayensu ko asalinsu

- Gwamnatin ta ce tun a shekarar 1974 gwamnatin jihar kamar sauran jihohi ta fara daukan dukkan dawainiyar makarantun kuma ta yi doka na mayar da su na gwamnati

Gwamnatin Jihar Kwara ta ce a yanzu dalibai musulmi mata suna iya saka hijabinsu a dukkan makarantun gwamnati da ke fadin jihar, The Punch ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan ta ki amincewa da ikirarin da wasu masu addinai suka yi na cewa su ke da wasu makarantu a jihar.

Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta
Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Rasa Rayuka Sakamakon Hatsarin Da Trela Dauke da 'Yan kasuwa 70 Ta Yi a Bauchi

Jihar fara kulawa da makarantun tun a shekarar 1974 kuma ita ke gudanar da dukkan harkoki da suka hada da daukan ma'aikata da biyansu don haka ta ki amincewa da ikirarin cewa wasu makaratun mallakar musulmi ne ko kiristoci yan mission.

Wannan na cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun sakataren gwamnatin Kwara, Farfesa Mamman Saba Jibril mai lakabin 'Wayar da kai game da 'makarantun mission' da Hijabi a Jihar Kwara.

Gwamnatin ta fitar da sanarwar bayan rikicin da ya barke tsakanin kirista da musulmi a jihar a ranar Laraba kan batun saka hijabi a wani makaranta da kirista ke ikirarin na yan mission ne.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban JAMB Kan Almundahar N900m

"Gwamnatin Kwara, kamar mafi yawancin jihohi fara daukan dawainiyar kula da makarantu da dama a 1974. Wasu makarantun a baya mallakar kungiyoyin addinai ne da masu zaman kansu a kasar. Amma tun daga lokacin gwamnati ke kula da dukkan dawainiyar makarantun da har yanzu ake cigaba da kula da su a matsayin makarantun gwamnati. Kuma akwai doka da ta bawa gwamnati wannan damar musamman Dokar Ilimi ta Jihar Kwara ta 1996 (CAP E1 of the Laws of Kwara State). Wannan dokokin sun fayyace komai game da matsayin makarantun kamar daukan malamai da dalibai. Wadannan makarantun gwamnati ne, na jama'a ne kuma dole su bi dokokin gwamnati," a wani sashi na sanarwar.

Kazalika, kotu ta yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa makarantun na musulmi ne ko na kirista kuma gwamnatin ta bar sunan wadanda suka kafa ne saboda karramawa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel