NDLEA: Ya kamata takardar shaidar rashin ‘shaye-shaye’ ta zama cikin sharudan daurin aure

NDLEA: Ya kamata takardar shaidar rashin ‘shaye-shaye’ ta zama cikin sharudan daurin aure

- Shugaban hukumar NDLEA ya ba iyaye shawarar yadda za a rage shaye-shaye

- Birgediya-Janar Buba Marwa ya bukaci a rika yin gwajin shaye-shaye kafin aure

- Buba Marwa ya na ganin hakan zai rage yawan masu amfani da kwayoyi sosai

Shugaban hukumar NDLEA mai yaki da masu safara da amfani da miyagun kwayoyi, Buba Marwa, ya yi kira ga iyaye game da aurar da ‘ya ‘yansu.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Birgediya-Janar Buba Marwa ya yi kira ga iyaye su rika neman takardar shaye-shaye kafin a daura wa yara aure.

Buba Marwa ya na so samari da ‘yan mata a Najeriya su rika gabatar da takardar shaida wanda za ta tabbatar da cewa ba su amfani da miyagun kwayoyi.

Janar Buba Marwa ya na ganin hakan zai taimaka wajen rage adadin ‘yan shaye-shaye a Najeriya.

KU KARANTA: Buba Marwa: NDLEA ta kama hodar ibilis ta N30bn daga Brazil

Buba Marwa yake cewa: “Wannan zai zama mataki na farko wajen rage amfani da miyagun kwayoyi da matsalolin tattalin arzikin da su ke jawo wa kasar.”

Shugaban na NDLEA ya bayyana haka ne a garin Ado-Ekiti a ranar Alhamis, 18 ga watan Maris, 2021, da ya gabatar da wata lacca da taken ‘A guji kwayoyi.’

A wajen laccar, Marwa ya koka da cewa cikin watanni biyu da su ka wuce, jami’an NDLEA sun kama miyagun kwayoyin da darajar su ya haura Naira Biliyan 60.

Janar Marwa ya bayyana halin shaye-shayen da kasar nan ta ke ciki a yau a matsayin abin damu wa.

KU KARANTA: Janar Marwa ya dage da yaki da shan kwaya a Najeriya

NDLEA: Ya kamata takardar shaidar rashin ‘shaye-shaye’ ta zama cikin sharudan daurin aure
Buba Marwa da Gwamnan Legas Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A Najeriya yau, babu kalubalen da ya zarce na shaye-shayen kwayoyi.” Inji shi. Sannan ya ce: “Idan aka rage samun kwayoyi, an yi maganin 50% na matsalar.”

Gwamnatin Ekiti ta shirya wannan taro wanda ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar.

Kun ji cewa ana zargin tsohon hadimin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari Okoi Obono-Obla da wani Mukarrabinsa da aikata wasu laifuffuka a gaban kotu.

Hukumar ICPC ta ce tsohon shugaban SPIP mai karbo kadarorin gwamnati da ke hannun barayi ya yi gaba da wasu daga cikin kudin kwangilar gyaran ofishinsa.

ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta koma kotu da Obono-Obla a makon nan.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel