Buba Marwa: NDLEA ta kama hodar ibilis ta N30bn da aka shigo da ita daga Brazil

Buba Marwa: NDLEA ta kama hodar ibilis ta N30bn da aka shigo da ita daga Brazil

- Hukumar NDLEA ta yi babban kamun wata hodar ibilis da aka shafe shekaru fiye da 15 ba'a kama mai yawanta ba a Nigeria

- Jami'an hukumar NDLEA sun kama wata mata dauke da hodar ibilis a filin saukar jirage na Murtala Muhammed da ke jihar Legas

- Wani jami'in hukumar NDLEA ya ce kudin muguwar hodar zai haura miliyan ashirin da daya da ta tsallake zuwa cikin kasa

NDLEA, hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nigeria, ta samu samu nasarar kama hodar ibilis ta biliyan N30 a Legas.

Jami'an hukumar sun kama hodar ibilis din ne a wurin wata mata mai suna Onyejegbu Ifesinachi, 'yar shekaru 33 da haihuwa.

Matar ta shiga hannu ne ranar 27 ga watan Janairu a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke jihar Legas bayan dawowar ta daga kasar Brazil.

Ifesinachi, mai sana'ar gyaran gashi a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, ta ce ta karbi aikin shigo da hodar zuwa Nigeriaakan miliyan biyu (N2,000,000).

KARANTA: Kura ta ci kura: An yi artabu tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga biyu a jihar Katsina

Buba Marwa: NDLEA ta kama hodar ibilis ta N30bn da aka shigo da ita daga Brazil
Buba Marwa: NDLEA ta kama hodar ibilis ta N30bn da aka shigo da ita daga Brazil @NDLEA
Asali: Twitter

KARANTA: Garkuwa da mutane: Hotunan dakarun soji mata zalla 300 da aka jibge a hanyar Abuja-Kaduna

Matashiyar ta bawa hukumar NDLEA sunayen sauran mutanen da suke aiki tare tare da bayyana cewa an umarceta ta mika kwayoyin ga wani mutum.

Wani jami'in hukumar NDLEA ya ce da hodar ibilis din ta tsallake, kudinta zai kai darajar biliyan ashirin da daya (N21bn).

A baya Legit.ng ta rawaito cewa sabon shugaban hukumar NDLEA mai yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya ce zai yi amfani da tsohon tsarin atisayen sweep (shara) domin magance matsalar fataucin miyagun kwayoyi a Nigeria.

Marwa ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja yayin wani taro da kwamandojin rundunar, inda aka raba sabbin motocin sintiri guda goma ga jihohi bakwai da NDLEA keda manyan hedikwatoci.

A cewar Marwa, an raba motocin ne a jihohin da suka hada da Abuja domin inganta aiyukan hukumar NDLEA a kokarinta na yakar tu'ammali da miyagun kwayoyi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel