Obono-Obla: Hukumar ICPC ta fadawa Alkali yadda tsohon Hadimin Buhari ya saci kudi

Obono-Obla: Hukumar ICPC ta fadawa Alkali yadda tsohon Hadimin Buhari ya saci kudi

- Hukumar ICPC ta sake gurfanar da Okoi Obono-Obla a wani kotu da ke Abuja

- Ana zargin tsohon hadimin Shugaban kasar ne da zargin karkatar da miliyoyi

- An gurfanar da Mr. Okoi Obono-Obla ne tare da hadiminsa, Aliyu Ibrahim jiya

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto cewa hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta koma kotu da Mista Okoi Obono-Obla.

Hukumar ta ICPC ta na zargin tsohon mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara, Okoi Obono-Obla, da laifuffuka biyar, daga ciki har da sata.

ICPC ta gurfanar da Obono-Obla ne tare da wani hadiminsa, Aliyu Ibrahim a babban kotun tarayya a Abuja.

Alkali Olukayode Adeniyi shi ne mai sauraron wannan kara. Kafin yanzu an gurfanar da wadanda ake zargi tare da Daniel Omughele a watan Junairu.

KU KARANTA: ICPC ta na neman hadimin Buhari da aka sallama 'ruwa a jallo'

Lauyoyin sun zargi Obono-Obla, Ibrahim, da darektan kamfanin ABR Global Petroleum Resources Limited, Omughele da laifuffuka har 10 a lokacin.

Da aka zauna a ranar Laraba, 17 ga watan Maris, 2021, lauyan hukumar ICPC, Olusola Bayeshea, ya bukaci a bada dama ya gyara tuhumar da su ke yi.

Ganin cewa wadanda ake zargi da laifin ba su ce komai ba, Alkali ya ba ICPC damar yin kwaskwarima a karar da ta shigar a kan mutanen biyu.

Bayan an yi gyara a laifuffukan da ake tuhumarsu da ita, wadanda ake zargin sun ce ba su aikata laifi ba.

KU KARANTA: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya sanar da Majalisa

Obono-Obla: Hukumar ICPC ta fadawa Alkali yadda tsohon Hadimin Buhari ya saci kudi
Okoi Obono-Obla Hoto: legit.ng
Asali: Facebook

ICPC ta na ikirarin Obono-Obla da Ibrahim sun karkatar da N10,174,000 daga cikin kudin kwangila N15,187,917 da hukumar NDIC ta biya a gyara ofishin SPIP.

Hukumar ta fada wa kotu cewa an biya wadannan kudi ne cikin asusun ABR Global Petroleum Resources Ltd, wanda Ibrahim shi ne darektan wannan kamfani.

A shekarar bara kun ji cewa tsohon shugaban kwamitin karbo kadarorin gwamnatin tarayya (SPIP), Okoi Obono-Obla, ya shigar da karar hukumar ICPC a kotu.

A lokacin, ICPC ta tuhumi Obono-Obla da karyar takardar makaranta da kuma bayar da alkaluman bogi ga gwamnati a kan kadarorin da ake karbo wa.

Buhari ya dakatar da bono-Obla ne bayan an kai ruwa rana a kan batun zarginsa da laifi da ake yi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng