NDLEA: Marwa zai farfado da tsohuwar rundunar atisaye domin yaki da kwaya a Nigeria

NDLEA: Marwa zai farfado da tsohuwar rundunar atisaye domin yaki da kwaya a Nigeria

- Buba Marwa, shugaban hukumar NDLEA, ya ce zai waiwayi tsohon tsarin da ya taimakawa gwamnatinsa ta mulkin soja a jihar Legas

- A lokacin da ya ke gwamna a Jihar Legas, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya yi suna wajen yaki da aikata laifuka manya da kanana

- Marwa ya sanar da cewa zai yi amfani da tsohon tsarin atisayen da ya bawa gwamnatinsa damar samun nasara sosai a bangaren tsaro

Sabon shugaban hukumar NDLEA mai yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya ce zai yi amfani da tsohon tsarin atisayen sweep (shara) domin magance matsalar fataucin miyagun kwayoyi a Nigeria.

Marwa ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja yayin wani taro da kwamandojin rundunar, inda aka raba sabbin motocin sintiri guda goma ga jihohi bakwai da NDLEA keda manyan hedikwatoci.

A cewar Marwa, an raba motocin ne a jihohin da suka hada da Abuja domin inganta aiyukan hukumar NDLEA a kokarinta na yakar tu'ammali da miyagun kwayoyi.

KARANTA: Ka daina shararawa 'yan Nigeria karya; Dan majalisa ya caccaki ministan Buhari

NDLEA: Marwa zai farfado da tsohuwar rudunar atisaye domin yaki da kwaya a Nigeria
NDLEA: Marwa zai farfado da tsohuwar rudunar atisaye domin yaki da kwaya a Nigeria (@Thecableng, @Daily_trust)
Asali: Twitter

An bayar da motoci kirar Hilux guda dai-dai ga jihohin Edo, Yobe, Sokoto, Nasarawa, Niger, Ogun, da Enugu yayin da aka bawa hedikwatar rundunar da ke Abuja guda biyu.

KARANTA: Hoton mace bakar fata zai maye gurbin na tsohon shugaban Amurka a jikin takardar Dala

Marwa ya fara kirkirar atisayen 'operaion sweep' a jihar Legas lokacin yana gwamnan mulkin soja domin yakar fashi da makami da sauran laifuka manya da kanana.

"Zamu yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro. Sabon tsarin da za'a bullo da shi zai bamu damar samun bayanan sirri cikin sauki da kwanciyar hankalin wanda ya bayar da bayanin. Irin hakan ya taimaka mana matuka a lokutan atisayen 'Operation sweep' a Legas.

"Jama'a suna jin tsoron bayar da bayanai akan 'yan ta'adda da masu laifi saboda suna tsoron cewa jami'an tsaro zasu tona musu asiri daga baya. Na san da hakan, shi yasa yanzu zan waiwayi kundina domin sake dawo da tsarin da ya taba taimaka mana sosai a baya," a cewar Marwa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel