Yanzu-Yanzu: Mutum 56 suna Amai da Fitsarin Jini Sakamakon Bullar Wata Sabuwar Cuta a Kano

Yanzu-Yanzu: Mutum 56 suna Amai da Fitsarin Jini Sakamakon Bullar Wata Sabuwar Cuta a Kano

- Kimanin mutane 56 suna amai da fitsarin jini a kauyen Gwangwan a jihar Kano

- Wasu mazauna kauyen sun ce mutane na cikin firgici sakamakon bullar cutar da suka ce bata jin magani

- Amma jami'an Asibiti a garin Rogo sun ce ba su da labarin bullar cutar a garin

A kalla mutane 56 a kauyen Gwangwan da ke jihar Kano suna amai da fitsarin jini sakamakon bullar wata bakuwar cuta a kauyen, Vanguard ta ruwaito.

Mutanen garin Gwangwan da ke karamar hukumar Rogo sun shiga rudani da firgici ganin halin da mara lafiyan suka shiga.

DUBA WANNAN: Hana Sa Hijabi: Sarkin Ilorin Ya Aike da Saƙo Ga Musulmi Da Kirista a Kwara

Yanzu-Yanzu: Mutum 56 suna Amai da Fitsarin Jini Sakamakon Bullar Wata Sabuwar Cuta a Kano
Yanzu-Yanzu: Mutum 56 suna Amai da Fitsarin Jini Sakamakon Bullar Wata Sabuwar Cuta a Kano. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Wani mazaunin kauyen mai suna Muhammad Tukur ya ce wuri shida a kauyen abin ya shafa inda kimanin mutane 56 sun kamu da bakuwar cutar tun bullar ta.

"Unguwannin da abin ya shafa sun hada da Unguwan Rijiyan Dadi, Gwanwan Gabas, Gwangwan Yamma, Unguwar Tsarmai, Gangare, da Unguwar Kofar Fada.

"Mun garzaya da akalla mutane 30 zuwa babban asibitin Rogo tun ranar da cutar ta bulla.

"Kawo yanzu, mutum daya ne kawai ya rasu sakamakon cutar. Mafi yawancin wadanda cutar ta kama suna ta korafi kan kudade da suke kashewa wurin yin magani," ya yi bayani.

KU KARANTA: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

Wani wanda kimanin mutum takwas suka kamu a gidansa ya ce ya kashe kimanin N100,000 wurin magani a asibitin Rogo da Gwarzo kuma har yanzu babu sauki.

Sai dai jami'an Asibitin Rogo wanda ba su son a fadi sunansu sun ce ba su da labarin bullar cutar.

Amma jami'in da ke kula da cututtuka masu yaduwa a Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano ya ce ma'aikatar ta samu labarin bullar cuta amma mutum hudu kadai suka kamu kuma an musu magani sun warke an sallame su.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magafuli ya rasu sakamakon ciwon zuciya kamar yadda mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan ta sanar.

Suluhu Hassan yayin jawabin da ta yi wa yan kasar kai tsaya ta kafafen watsa labarai, ta sanar da rasuwarsa inda ta ce za a yi zaman makoki na kwanaki 14 a kasar.

A cewar mataimakiyar shugaban kasar, Mr Magafuli ya rasu ne a yammacin ranar Laraba 17 ga watan Maris na shekarar 2021 a asibiti a Dar es Salaam.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel