Hana Sa Hijabi: Sarkin Ilorin Ya Aike da Saƙo Ga Musulmi Da Kirista a Kwara

Hana Sa Hijabi: Sarkin Ilorin Ya Aike da Saƙo Ga Musulmi Da Kirista a Kwara

- Mai martaba Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari ya shawarci musulmi da kirista a jihar Kwara su rungumi zaman lafiya

- Sarkin, cikin sanarwar da ya fitar ya bukaci mabiya addinan biyu su mutunta doka da oda kan batun saka hijabi a wasu makarantun da gwamnati ke kula da su

- Sarkin na Ilorin ya kuma yi kira ga shugabannin mabiya addinan biyu su rika tunatar da mabiyansu yin biyayya ga doka da zaman lafiya

Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, Sarkin Ilorin kuma shugaban kwamitin masu sarauta na jihar Kwara, ya bukaci musulmi da kirista na jihar su rungumi zaman lafiya.

Sulu-Gambari ya yi wannan rokon ne a Ilorin, ranar Laraba cikin wata sanarwa da kakakinsa Mr AbdulaAzeez Arowona ya fitar, The Punch ta ruwaito.

Hana Sa Hijabi: Sarkin Ilorin Ya Bukaci Musulmi Da Kirista Su Rungumi Zaman Lafiya
Hana Sa Hijabi: Sarkin Ilorin Ya Bukaci Musulmi Da Kirista Su Rungumi Zaman Lafiya. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

Sarkin mai sanda mai daraja ta daya ya shawarci mabiya addinan biyu su cigaba da zama lafiya da juna domin samun zaman lafiya da cigaba a jihar.

A cewar sanarwar, basaraken ya bayyana rikicin da aka yi kan saka hijabi a makarantun gwamnati 10 a jihar a matsayin abinda bai dace ana ja-in-ja kansa ba.

"Kada wata kungiya ko mutum ya dau doka a hannunsa, an san Ilorin da zaman lafiya a duk kasar nan. Mu cigaba da zama lafiya duba da cewa doka ta raba gardama kan batun.

KU KARANTA: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

"Babu fada tsakanin musulmi da kirista. Mu guje wa duk wani rikicin addini. Addinin musulunci da kirista duk zaman lafiya suke koyarwa. Ya kamata mu gujewa rabuwar kai da kiyayya," in ji Sarkin.

Ya yi kira ga shugabannin addinin biyu su yi wa mabiyansu huduba na cewa su yi wa dokoki biyayya a duk lokacin da suke harkokinsu.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magafuli ya rasu sakamakon ciwon zuciya kamar yadda mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan ta sanar.

Suluhu Hassan yayin jawabin da ta yi wa yan kasar kai tsaya ta kafafen watsa labarai, ta sanar da rasuwarsa inda ta ce za a yi zaman makoki na kwanaki 14 a kasar.

A cewar mataimakiyar shugaban kasar, Mr Magafuli ya rasu ne a yammacin ranar Laraba 17 ga watan Maris na shekarar 2021 a asibiti a Dar es Salaam.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel