Yanzu-Yanzu: Shugaban Kasar Tanzania John Magafuli ya rasu

Yanzu-Yanzu: Shugaban Kasar Tanzania John Magafuli ya rasu

- Allah ya yi wa Shugaban Kasar Tanzania, John Pombe Magafuli rasuwa a ranar Laraba 17 ga watan Maris 2021

- Mista Magafuli ya rasu ne a Dar es Salaam sakakamon ciwon zuciya kamar yadda mataimakiyarsa Suluhu Hassan ta sanar

- An haifi Magafuli a ranar 29 ga watan Oktoban 1959, ya girma a wani kaye da ke arewa maso yammacin yankin Chato da ke kusa da Tafkin Victoria

Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magafuli ya rasu sakamakon ciwon zuciya kamar yadda mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan ta sanar.

Suluhu Hassan yayin jawabin da ta yi wa yan kasar kai tsaya ta kafafen watsa labarai, ta sanar da rasuwarsa inda ta ce za a yi zaman makoki na kwanaki 14 a kasar.

Yanzu-Yanzu: Shugaban Kasar Tanzania John Magafuli ya rasu
Yanzu-Yanzu: Shugaban Kasar Tanzania John Magafuli ya rasu. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

A cewar mataimakiyar shugaban kasar, Mr Magafuli ya rasu ne a yammacin ranar Laraba 17 ga watan Maris na shekarar 2021 a asibiti a Dar es Salaam.

An shafe makonni ba a gansa a fili ba hakan ya tilastawa yan adawa fara tambaya a game da shi.

Marigayin, mai shekaru 61 ya rasu ne bayan makonni aka zargin ya kamu da kwayar cutar korona.

DUBA WANNAN: Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

Magafuli bai amince a rufe makarantu, ma'aikatu da sauran harkoki ba kamar yadda aka yi a wasu kasashe inda ya ce mutane su koma masallatai da coci-coci su yi addu'o'i domin cutar ba za ta samu duk wanda ya rungumi addua ba.

Hakazalika, bai gamsu da ingancin rigakafin annobar ta korona ba don haka ya ce gwamnatinsa ba ta da wani tsari na siyan alluran rigakafin.

"Mu yan Tanzania ba zamu rufe kan mu ba, kuma ba zan sanar da ko rana guda na zaman gida ba domin Ubangijin mu rayayye ne, kuma zai cigaba da kare mu a Tanzania," kamar yadda marigayin shugaban ya shaidawa jama'a.

An haife shi a ranar 29 ga watan Oktoban 1959, ya girma a wani kaye da ke arewa maso yammacin yankin Chato da ke kusa da Tafkin Victoria

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel