Wata biyar basu biyani albashi ba, Baturen Kocin Kano Pillars ya yi murabus

Wata biyar basu biyani albashi ba, Baturen Kocin Kano Pillars ya yi murabus

- Bayan dan karamin lokaci da fara aiki, kocin Kano Pillars ya yi murabus

- Kocin wanda dan asalin Faransa ne ya yi kukan rashin biyansa albashi

- Ya ce yana bin kungiyar miliyoyin kudi kuma basu biya shi ba

Kungiyar kwallon Kano Pillars da Baturen Kocinta, Lionel Soccoia, sun raba jiha bayan ya ajiye aikinsa sakamakon rashin biyansa albashi da yi masa shisshigi cikin lamuran aikinsa.

A cewar Kocin, bashin da yake bin kungiyar kwallon $25,000, rahoton Vanguard.

"Ina sanar da ku cewa na ajiye aikina matsayin Kocin Kano Pillarsa daga yanzu," ya bayyana a wasikar murabus dinsa.

"Kano Pillars ta saba kwantiragina ta hanyar kin biya na albashin watanni biyar, hakan na nufin cewa babu wata alaka tsakani na da ita."

Bayan haka, kocin ya ce shugaban kungiyar ya na yi masa shisshigi cikin aikinsa ta hanyan zaba masa yan wasa.

"An dade ana saba alkawuran da aka yi mai. Hakan yan tsananta rayuwar iyalinsa. Da ni ne, da tuni na tafi," Wani wakilinsa ya bayyana.

KU KARANTA: Yar'adua, Gaddafi da sauran shugabannin kasashen Afrika 16 da suka mutu kan mulki

Wata biyar basu biyani albashi ba, Baturen Kocin Kano Pillars ya yi murabus
Wata biyar basu biyani albashi ba, Baturen Kocin Kano Pillars ya yi murabus Credit: @vanguardngr
Source: Twitter

KU DUBA: Bayan watanni 6, Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya

A bangare guda, a shekarar 2019 ne gwamnatin jihar ta aurar da mutane 1,500 a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar.

An sanar da hakan ne a cikin wani jawabi dauke da sa hannun kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammed Garba zuwa ga manema labarai a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairu.

Majalisar ta kuma amince da sakin naira miliyan 274.2 ga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars domin tafiyar da harkokin kakar wasannin kwallon kafa ta 2020/2021 yadda ya kamata.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel