Yar'adua, Gaddafi da sauran shugabannin kasashen Afrika 16 da suka mutu kan mulki

Yar'adua, Gaddafi da sauran shugabannin kasashen Afrika 16 da suka mutu kan mulki

Shugabannin kasashen Afrika da dama sun mutu kan mulki kafin karewar wa'adinsu. Yayinda wasu kashesu akayi, wasu sun mutu ne sakamakon cuta da suke fama da shi.

Na kusa-kusa shine shugaban kasar Tanzaniya, John Magufuli, wanda ya mutu ranar Laraba, 17 ga watan Maris, 2021.

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa nahiyar Afrika ta yi rashin babban jagora.

Yar'adua, Gaddafi da sauran shugabannin kasashen Afrika 16 da suka mutu kan mulki
Yar'adua, Gaddafi da sauran shugabannin kasashen Afrika 16 da suka mutu kan mulki
Asali: UGC

DUBA NAN: Bayan watanni 6, Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya

Legit ta tattaro muku jerin shugabannin kasa a Afrika da suka mutu kan mulki:

1. John Magufuli na kasar Tanzaniya: Ya mulki kasar na tsawon shekaru shida kuma ya mutu sakamakon ciwon zuciya a Maris 2021

2. Pierre Nkurunziza na kasar Burundi: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 15, Ya mutu sanadiyar bugun zuciya Yunin 2020

3. Michael Sata na kasar Zambiya: Ya mutu Oktoba 2014, ba'a bayyana abinda yayi sanadiyar mutuwarsa ba.

4. Meles Zenawi na kasar Ethiopia: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 21 daga 1991 zuwa 2012. Ya mutu a Agustan 2012. ba'a bayyana abinda yayi sanadiyar mutuwarsa ba.

5. John Atta Mills na kasar Ghana: Ya mulki Ghana daga 2009 zuwa lokacin da ya mutu sanadiyar bugun jini da cutar daji a 2012.

6. Bingu wa Mutharika na kasar Malawi: Ya mulki kasar na shekaru takwas kuma ya mutu a sanadiyar bugun zuciya 2012.

7. Malam Bacai Sanha na Guinea-Bissau: Ya mulki kasar na tsawon shekaru hudu kacal kuma ya mutu sanadiyar cututtuka da dama a 2021

8. Moammar Gadhafi na kasar Libya: Yan tawaye sun kashe shi bayan mulki tsawon shekaru 42 a Libya a shekarar 2011.

9. Umaru Musa Yar’Adua na Najeriya: Ya mulki Najeriya na tsawon shekaru uku kacal kuma ya mutu a sanadiyar cutar pericarditis a shekarar 2010

10. Joao Bernardo Vieira na Guinea-Bissau: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 31 kuma an kashe shi a watan Maris na 2009.

DUBA NAN: Jerin Jihohin da ke da Mafi Yawa da Karancin Rashin Aikin Yi a Nigeria

11. Omar Bongo na kasar Gabon: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 42 kuma ya mutu a Yunin 2009 sanadiyar cutar dajin hanji.

12. Lansana Conte na kasar Guinea: Ya yi fama da cutar Siga kuma ya mulki kasar na tsawon shekaru 24. Ya mutu a 2008.

13. Levy Mwanawas na kasar Zambiya: Ya mutu yayin wa'adinsa na biyu a Agustan 2008

14. Gnassingbe Eyadema na kasar Togo: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 38 kuma ya mutu a 2005 sanadiyar bugun zuciya.

15. Muhammad Egal na kasar Somaliya: Ya mutu a 2002 ana yi masa aikin Tiyata a kasar Afrika ta kudu.

16. Laurent Kabila na kasar Congo: Ya mutu shekarar 2001 lokacin wani dogari ya bindigeshi a fadar shugaban kasa

17. Ibrahim Maniassara na kasar Nijar: Wasu da ake zargin dogarenshi ne suka bude masa wuta har lahira a shekarar 1999

18. Sarkin Maroko, Hassan II: Ya mulki Maroko na tsawon shekaru 38 kuma jinin Manzon Allah (S.A.W) ne. Ya mutu a 1999.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel