Da duminsa: Bayan watanni 6, Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya

Da duminsa: Bayan watanni 6, Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta dawo gida Najeriya bayan watanni shida a birnin Dubai, kasar haddadiyar daular Larabawa.

Legit Hausa ta samu labari daga majiya mai karfi cewa Aisha tana fadar shugaban kasa da ranan nan.

Uwargidar shugaban kasan ta tafi Dubai ne tun bayan auren diyarta, Hanan, a Satumban 2021.

An samu labarin cewa ta dawo kasar da daren Laraba.

Da duminsa: Bayan watanni 6, Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya
Da duminsa: Bayan watanni 6, Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya Credit: @aishambuhari
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel