Kano ta amince da naira miliyan 245 domin yin auren mata da yawa
- Gwamnatin Kano ta ware naira miliyan 245 don gudanar da auren mata da yawa a fadin jihar
- Har ila yau ta amince da sakin naira miliyan 274.2 ga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars
- Kwamishinan labarai na jihar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar
Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da naira miliyan 245 don gudanar da auren mata da yawa a fadin jihar.
A shekarar 2019 ne gwamnatin jihar ta aurar da mutane 1,500 a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar.
An sanar da hakan ne a cikin wani jawabi dauke da sa hannun kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammed Garba zuwa ga manema labarai a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairu.
KU KARANTA KUMA: Fasto Adeboye ya yi hasashen lokacin da ta’addanci zai zo karshe a Nigeria
Majalisar ta kuma amince da sakin naira miliyan 274.2 ga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars domin tafiyar da harkokin kakar wasannin kwallon kafa ta 2020/2021 yadda ya kamata.
A cewar sanarwar, majalisar zartarwar ta jihar Kanon ta kuma amince da fitar da naira miliyan 29.3 domin aikin allurar rigakafi na shekarar 2020/2021 a tsakanin alumomin makiyaya.
An dakatar da shirin tsawon shekaru uku da suka gabata saboda hatsarin kiwon lafiya da asarar tattalin arziki da ke damun wasu al'ummomin jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Rikicin APC a Kwara: An kwantar da jiga-jigan jam’iyyar 5 bayan musayar naushi da jefe-jefen kujeru da suka yi
Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa majalisar ta amince da sama da naira biliyan 1 da miliyan 200 don kammala aikin gyaran titin Ahmadu Bello Way.
Sai kuma naira miliyan 212.9 da aka amince da shi don sake gina dakunan kwanan mata na Dangote a jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano da ke Wudil.
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Kano ta ce ta dame mabarata 500 kan laifin saba dokan hana barace-barace a kan hanya a cikin jihar.
Kwamishanar harkokin matan jihar, Dr Zahra’u Muhammad-Umar, ya bayyana hakan yayinda ake mayar da mabaratan jihohinsu na asali jiya, Leadership ta ruwaito.
Dr Zahra'u ta ce an damke mabaratan ne a cikin birnin Kano kuma yawancinsu mata ne da yara.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng