Shan giya haramun ne a Jigawa: Kwamandan Hisbah yayinda suka damke jarkan Burkutu da kwalabe 364

Shan giya haramun ne a Jigawa: Kwamandan Hisbah yayinda suka damke jarkan Burkutu da kwalabe 364

- Hukumar Hisbah a jihohin Arewa na cigaba da dabbaka dokokin addinin Musulunci

- A Jigawa, hukumar ta lalata dubunnan kwalaben giya da ta kama

- Hukumar ta jaddada cewa an haramta shan giya a ko ina a fadin jihar

Hukumar Hisbah a jihar Jigawa ta damke jarkan barasan gargajiya wanda aka fi sani da Burkuku guda daya a karamar hukumar Kazaure.

Kwamandan Hisban jihar, Malam Ibrahim Dahiru, ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Dutse cewa hakazalika hukumar ta damke kwalaben giya 364.

Dahiru ya ce an damke wadannan barasa cikin wata mota kirar Toyota Corona misalin karfe 9 na safiyar ranar Laraba, 17 ga watan Maris, 2021.

Ya yi bayanin cewa a kwanakin nan hukumar ta fasa kwalaben giya 2,875 da galolin burkutu hudu a wuraren daban-daban na jihar.

Kwamandan ya kara cewa an fasa kwalaben ne bayan samun umurnin kotu saboda shan barasa haramun ne a fadin jihar.

Saboda haka ya yi kira ga al'ummar jihar su taimakawa hukumar da labarin duk inda suka ga ana alfasha.

KU KARANTA: Jerin Jihohin da ke da Mafi Yawa da Karancin Rashin Aikin Yi a Nigeria

Shan giya haramun ne a Jigawa: Kwamandan Hisbah yayinda suka damke jarkan Burkutu da kwalabe 364
Shan giya haramun ne a Jigawa: Kwamandan Hisbah yayinda suka damke jarkan Burkutu da kwalabe 364
Source: Facebook

KU KARANTA: Sarkin Ilorin Ya Aike da Saƙo Ga Musulmi Da Kirista a Kwara

A wani labari kuwa, Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar kano, ya ce mazauna jihar sun fi yadda da jami'an Hisbah a kan 'yan sanda.

Shekarau ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

Ya jaddada bukatar samar da 'yan sandan yanki domin shawo kan matsalar tsaron da ya addabi kasar nan.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel