Mazauna Kano sun fi son jami'an Hisbah akan 'yan sanda, Shekarau

Mazauna Kano sun fi son jami'an Hisbah akan 'yan sanda, Shekarau

- Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya ce jama'ar jihar Kano sun fi yadda da 'yan Hisbah fiye da 'yan sanda

- Shekarau ya sanar da hakan ne yayin magana a kan matsalar tsaron da ta addabi kasar nan baki daya

- Tsohon sanatan ya ce akwai bukatar a samar da jami'an tsaron yanki domin an fi yadda dasu a kan 'yan sanda

Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar kano, ya ce mazauna jihar sun fi yadda da jami'an Hisbah a kan 'yan sanda.

Shekarau ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

Ya jaddada bukatar samar da 'yan sandan yanki domin shawo kan matsalar tsaron da ya addabi kasar nan.

"Tsaro alhakin kowa ne kuma hakan yasa ake bukatar 'yan sandan yanki," yace.

KU KARANTA: Bidiyon sankama daloli: Ganduje ya bukaci sauya rantsuwa da shaidu a gaban kotu

Mazauna Kano sun fi son jami'an Hisbah akan 'yan sanda, Shekarau
Mazauna Kano sun fi son jami'an Hisbah akan 'yan sanda, Shekarau. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"A cikin shekara daya zuwa biyu da aka samar da hukumar Hisbah, mun yi nasarar shawo kan kusan kashi 90 na matsaloin da ke damun al'ummarmu kuma mun samu zaman lafiya. Tabbas wannan na daga cikin abinda Kano ke jin dadi yanzu.

"Ka tambaya kowa a Kano yau, jama'a sun fi son zuwa ofishin Hisbah domin kai rahoton duk abinda ya faru a al'umma fiye da zuwa wurin 'yan sanda ko kuma kotu."

KU KARANTA: Bidiyo: Sunday Igboho ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga 'yan sanda, soja da DSS

A wani labari na daban, Aliyu Mohammed, shugaban sashi na 4 ta rundunar sintirin hadin guiwa a iyakokin kasar nan ta kwastam a arewa maso yamma, ya ce ya taba baiwa 'yan bindiga buhu bakwai na shinkafa domin samun 'yancinsa.

A yayin jawabi ga manema labarai a Katsina a ranar Talata, Mohammed ya ce lamarin ya auku ne a karamar hukumar Dutsinma ta jihar.

Mohammed yana tsokaci ne a kan kalubalen da jami'an hukumar kwastam ke fuskanta yayin sauke hakkin dake kansu, The Cable ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel