NDDC ta fallasa Gwamnonin N/Delta 9, an ba kowace Jiha N100m a matsayin tallafin COVID-19

NDDC ta fallasa Gwamnonin N/Delta 9, an ba kowace Jiha N100m a matsayin tallafin COVID-19

- NDDC ta na ikirarin ta batar da Naira Biliyan 6 wajen bada tallafin Coronavirus

- Sanatoci za su binciki Gwamnoni bayan an ce an ba kowace Jihar N100m

- Majalisar Dattawa ta ce sam ba ta samu labarin Gwamnoni sun raba tallafin ba

Kwamitin sauraron korafi na majalisar dattawa ta ce za ta binciki rawar da gwamnonin Neja-Delta su ka taka a wajen awon gaba da kudin NDDC.

A ranar Talata, 16 ga watan Maris, 2021, jaridar Punch ta rahoto majalisar dattawan ta na cewa binciken na ta zai iya kai wa ga gwamnonin yankin.

Ana zargin kowane daga cikin wadannan gwamnonin jihohi su tara sun karbi N100m daga hannun NDDC mai kula da cigaban yankin mai arzikin mai.

Rahoton ya ce kwamitin ya kuma ba shugaban rikon kwarya na NDDC, Effiong Akwa wa’adin sa’o'i 48 ya tattaro mata tsofaffin shugabannin hukumar.

KU KARANTA: Mukarrabin Pondei, ya yi murabus bayan Mai gidansa ya sume a Majalisa

Idan har Effiong Akwa bai iya kawo Daniel Pondei da ‘yan majalisar sa ba, majalisar dattawan ta yi barazanar za ta ba ‘yan sanda umarnin su cafke mata shi.

Ayo Akinyelure ya ce, “Mun riga mun duba yadda za a bada umarnin kama shi, mun yi 95% na aikin.”

“Mu na fito da barazanar kama shugaban rikon kwaryar, sai shugaban na NDDC ya zo ofishina, ya yi mani bayanin yadda aka batar da kudin da fatar-baki.”

“Su na ikirarin an ba kowane gwamna daga cikin gwamnonin Neja-Delta tara kudi Naira miliyan 100.”

KU KARANTA: An bada umarnin kama shugaban NDDC saboda lakume tallafin COVID-19

NDDC ta fallasa Gwamnonin N/Delta 9, an ba kowace Jiha N100m a matsayin tallafin COVID-19
Majalisar Dattawa Hoto: NgrSenate
Asali: UGC

Ya ce: “Sai mu ka ce su rubuta takarda, su yi wannan bayani kafin ranar 15 ga watan Maris, ranar Litinin kenan, amma har yau (Talata), ba mu ga komai ba.”

Sanata Ayo Akinyelure ya ce ba za a birne batun ba, ya ce dole majalisar dattawa ta binciki yadda aka batar da wannan kudin tallafin COVID-19 da NDDC ta bada.

Dazu kun samu labari majalisar Najeriya za ta kawo dabarar da za tayi maganin kunnen-kashin da Shugaban kasa yake yi idan an aika masa goron gayyata.

Watakila sabon kudirin zai raba gardama tsakanin ‘yan majalisar tarayya da shugaban Najeriya.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel