Majalisar dattawa ta bada umarnin kame shugaban NDDC saboda cinye tallafin Korona N6.25bn

Majalisar dattawa ta bada umarnin kame shugaban NDDC saboda cinye tallafin Korona N6.25bn

- Majalisar dattawa ta bada umarnin kwamushe shugaban NDDC da laifin salwantar da kudi

- Majalisar a baya ta umarci ya zo ya bada bayanin yadda ya salwantar da kudaden amma ya ki

- A halin yanzu Sufeto-janar na 'yan sanda ne zai kamo shi ya kawo shi gaban majalisar a watan gobe

Kwamitin majalisar dattijai kan da'a, gata da kuma koke-koken jama'a, ya bayar da sammacin kame kan mai rikon kwarya na Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Effiong Okon Akwa, saboda kin mutunta gayyatar kwamitin.

Kwamitin, a lokuta daban-daban, ya gayyaci shugaban NDDC da ya ba da bayani kan Naira biliyan 6.2 da aka kashe na kwamitin tallafin COVID-19, Daily Trust ta ruwaito.

Jin haushin rashin zuwan shugaban NDDC din a zaman da ta yi a ranar Litinin, Kwamitin, karkashin jagorancin Sanata Ayo Akinyelure (PDP Ondo ta Tsakiya), sun yanke shawara cewa Majalisar Dattawa za ta tuntubi Sufeto-Janar na ’Yan sanda ya kamo shi.

Za a baiwa Sufeto-janar ya kamo hugaban NNDC ya kawo shi gaban kwamitin ba tare da saurarawa ba a ranar 9 ga watan gobe.

KU KARANTA: Gumi: ‘Yan bindigan da na hadu da su sun musanta sace daliban Kagara

Majalisar dattawa ta bada umarnin kame shugaban NDDC saboda cinye tallafin Korona N6.25bn
Majalisar dattawa ta bada umarnin kame shugaban NDDC saboda cinye tallafin Korona N6.25bn Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Sanata Akinyelure ya ce:

“Bayan ya gayyaci shugaban hukumar ta NDDC har sau hudu ba tare da girmama gayyatar ba, wannan kwamitin ba shi da wani zabi da ya wuce kiran sashin kundin tsarin mulki da abin ya shafa don sammacin kama duk wanda ya kasance shugaban hukumar a yanzu.
“Takardar karar da wani jami’in yada labarai ya shigar kan hukumar kan zargin barnatar da N6.2bn na tallafin COVID-19 a shekarar da ta gabata yana da girma kuma yana da nauyi a yi watsi da shi.
"Don cimma wannan, tsarin da tsarin mulkin da ake bukata na wannan kwamitin za su bi wajen tabbatar da cewa Sufeto Janar na 'yan sanda ya gabatar da shugaban NDDC a gabanta a ranar 9 ga Maris, 2021 lokacin da zama na gaba zai gudana."

NDDC, a karkashin korarren Farfesa Daniel Pondei karkashin jagorancin kwamitin rikon kwarya (IMC), ta yi ikirarin kashe N6.25bn na tallafin COVID-19 a shekarar 2020 a tsakanin jihohin tara mai.

Amma Shugaban Kwamitin Rarrabawa na COVID-19 na hukumar, Ambasada Sobomabo Jackrich, a cikin wata takardar koke da aka aika wa kwamitin, ya ce ba a kashe ko sisin kwabo ba don wannan dalili ta IMC na Hukumar a lokacin.

KU KARANTA: Tsadar kudin wutan lantarki: Muna biyan ninki ukun abinda muke biya a baya, 'yan Najeriya

A wani labarin, Majalisar dattijai, a ranar Laraba, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da, cikin gaggawa, ya sanya dokar ta baci kan tsaro sakamakon sace ma’aikata da dalibai a wata makaranta a Niger.

Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Muhammed Sani Musa (APC, Neja) ya gabatar wanda ya ja hankalin abokan aikinsa kan sace wasu dalibai da ma’aikatan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kagara, Jihar Neja, da misalin karfe 2 na daren Laraba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel