Mukarrabin Pondei, Olomu Micheal, ya yi murabus daga ma’aikatar NDDC

Mukarrabin Pondei, Olomu Micheal, ya yi murabus daga ma’aikatar NDDC

- Yayin da ake binciken zargin badaka a Ma’aikatar NDDC, an samu sabon labari

- Olomu Micheal ya aika takardar murabus, ya ce lokaci ya yi da zai ajiye aikinsa

- Micheal Hadimi ne na Shugaban NDDC watau Farfesa Kemeberadikumo Pondei

Olomu Micheal, babban mai taimakawa shugaban NDDC, Farfesa Kemeberadikumo Pondei, ya rubuta takardar murabus, ya ajiye aiki a ma’aikatar.

Mista Olomu Micheal babban mai ba shugaban NDDC shawara ne wurin ayyuka na musamman. Yanzu haka ana binciken zargin badakala a ma'aikatar kasar.

Micheal ya ce lokaci ya yi da zai bar aiki da NDDC mai kula da cigaban yankin Neja-Delta, jaridar PM News ra rahoto Micheal ya na cewa ya yi wannan ne domin kansa.

A cewar tsohon hadimin, ya yi wa NDDC kokari a lokacin da ya ke aiki da shugaban ma’aikatar. Micheal ya yi duk wannan bayani ne a wasikar ajiye aikin da ya rubuta.

Mai bada shawarar ya rubuta takardar murabus ne tun a ranar 20 ga watan Yuli, amma sai a ranar Alhamis aka samun labarin ya ajiye wannan aiki mai tsoka.

KU KARANTA: Ta'adin da ake tafkawa a NDDC ta sa na ajiye aiki na - Kwankwaso

Mukarrabin Pondei, Olomu Micheal, ya yi murabus daga ma’aikatar NDDC
Farfesa Kemeberadikumo Pondei
Asali: UGC

“Ina so in sanar da matakin da na dauka na barin aiki na a matsayin babban mai bada shawara wajen ayyuka na musamman I a ma’aikatar NDDC.”

Wasikar ta kara da cewa: “Wajen rike kujerar wannan ofis, na yi bakin kokarina, na yi wa ma’aikatar aiki tukuru, na sauke nauye-nauyen da ke kai na.”

“Na dauki matakin cewa abin da zai fi mani shi ne in yi sallama a wannan lokaci.” Inji Olomu Micheal.

Olomu Micheal ya godewa maigidansa, Farfesa Kemeberadikumo Pondei da ya ba shi damar yin aiki a karkashinsa.

Haka zalika Micheal ya mika godiya ga ma’aikatar ta Neja-Delta da damar da ya samu yayin da ya rjarraba sa’arsa a wani aiki a wani wuri na dabam.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel