Kudiri zai ba Majalisa karfin sauke Shugaban kasa idan ya yi taurin-kan amsa gayyatarsu

Kudiri zai ba Majalisa karfin sauke Shugaban kasa idan ya yi taurin-kan amsa gayyatarsu

- Ana samun sa-in-sa tsakanin ‘Yan Majalisar Tarayya da Shugaban kasar Najeriya

- ‘Yan Majalisa su kan aikawa Shugaban kasa goron gayyata, amma ya ki amsawa

- Majalisa ta kawo wani kudirin da zai wajabtawa Shugaban kasa amsa gayyatarta

Jaridar The Cable ta rahoto cewa kudirin da zai ba majalisar tarayya karfin ikon gayyatar shugaban kasa zuwa gabanta, ya na cigaba da samun shiga.

Wannan kudiri da wani ‘dan majalisa mai wakiltar yankin jihar Edo, Hon. Sergius Ogun, ya gabatar, ya zarce mataki na biyu a zauren majalisar tarayyar.

Honarabul Sergius Ogun ya na kokarin yi wa tsarin mulki da dokar Najeriya garambawul.

Idan wannan kudiri ya samu shiga, majalisa za ta iya tursasa shugaban kasa ya bayyana a gabanta domin ya amsa duk tambayoyin da aka bijiro masa.

KU KARANTA: Malami ya ce Buhari bai zai bayyana gaban 'Yan Majalisa ba

Wannan kudiri zai ba har ‘yan majalisar dokoki gayyatar gwamnonin jihohinsu, su yi masu bayanai a duk lokacin da aka ga cewa akwai bukatar ayi hakan.

Ko da kudirin bai yi bayanin hukuncin da za a dauka a kan wanda ya saba wa majalisar ba, Sergius Ogun ya ce hakan zai kai ga tsige mai mulki daga kujera.

Idan kudirin ya zama doka, majalisar tarayya za ta iya aika wa shugaban kasa goron gayyata domin ya yi bayani a kan sha’anin tsaro ko makamancin haka.

Da aka tambayi ‘dan majalisar tarayyar, sai ya ke cewa: “Ba a zayyana hukuncin da za a zartar ba, amma hakan za ta iya yiwuwa (watau a tsige mutum daga ofis).”

KU KARANTA: Majalisa ta janye gayyatar da ta aikawa Shugaban kasa

Kudiri zai ba Majalisa karfin sauke Shugaban kasa idan ya yi taurin-kan amsa gayyatarsu
Shugaban kasa Buhari a gaban 'Yan Majalisa
Source: UGC

“Idan irin wannan ya shiga cikin dokar kasa, idan aka samu wanda ya cije, ya saba doka, ya zama za a iya sauke shi daga kujerar da yake kai.” Inji Ogun.

A bangare guda, idan za ka tuna, an ji Abubakar Malami ya yi magana a kan tirka-tirka da makomar tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya ce dokar kasa da tsarin aiki ne za su yi tasiri a bincikensa da ake yi.

AGF din ya ki cewa komai a game da shirin shigar da karar Ibrahim Magu a gaban Alkali.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel