Bayan shekaru 10 su na neman haihuwa, Allah ya ba ma’auratan da su ka yi hakuri tagwaye

Bayan shekaru 10 su na neman haihuwa, Allah ya ba ma’auratan da su ka yi hakuri tagwaye

- Bayan shekaru 10 da aure, a karshe wasu ma’aurata sun samu karuwar ‘ya ‘ya

- Ma’auratan sun shafe shekaru su na ta jiran tsammani, sai ga arzikin ‘yan biyu

- Sanarwar ta fito ne ta bakin wata Miss Ifeoma Uchenna a shafinta na Facebook

Wata Baiwar Allah a Najeriya ta samu tagwaye bayan shekara da shekaru ta na neman samun ‘ya ‘ya.

Wannan mata ta samu haihuwa ne shekaru 10 da yin aurenta, bayan ta shafe tsawon lokaci ta na rokon Ubangiji ya ba ta ‘ya ‘ya.

Labarin haihuwar wannan mata ya zo ne ta bakin wata ‘diyarta, Ifeoma Uchenna a kafar sadarwa na zamani na Facebook.

Uchenna ta wallafa hotunan matar a lokacin da ta yi nauyi a shafin Facebook, ta na cewa: “Shakka babu, babu abin da ya gagari Ubangiji.”

KU KARANTA: Mata ta mutu wajen haihuwa bayan fasto ya haramta ayi mata aiki

“Bayan shekaru goma da yin aure, a karshe Ubangiji ya amsa addu’ar goggo na da mai gidanta, ya ba su setin tagwaye.” Inji Uchenna.

"Ina mai matukar murna da godiya ga Ubangiji." inji goggon wadannan ‘yan biyu.

Bisa dukkan alamu mahaifiyar tagwayen ta sauka lafiya. Mutane a shafin Facebook sun shiga taya Ifeoma Uchenna murnar wannan karu wa.

Samuel Emmy ya ce: "Ina taya ku murna. Gaskiya ne, babu abin da ya gagari Ubangiji.”

KU KARANTA: Likita ya hana mai shekaru 36 haihuwa, bayan ta haifi 'ya'ya 44

“Ina taya ku murna mutanena.” Inji Wisdom Jacob.

Shi Injiniya Ima Onoyom Ita cewa ta yi: "Ina taya ki murna masoyiya, na yi maki murna.”

A kwanakin baya kun ji labarin wata matar aure da ta shafe shekara bakwai tana neman haihuwa, sai aka ji ta mutu bayan ta haifi 'yan hudu.

Allah ya karbi rayuwar wannan Baiwar Allah da ta haifi jariran 'yan mata uku da namiji daya.

'Yar uwarta ta wallafa labarin mutuwar ta a shafinta na Facebook, mutane sun ji zafin wannan mutuwa bayan jama'a sun yi ta farin cikin haihuwar ta.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel