Mata ta mutu wajen haihuwa bayan fasto ya ce haramun ne yin tiyata

Mata ta mutu wajen haihuwa bayan fasto ya ce haramun ne yin tiyata

Wata mata ta rasa ranta wajen haihuwa bayan da fasto ya sanar da su cewa haramun ne yin tiyata don cire da. Kamar yadda wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ya sanar, mijin marigayiyar abokinsa ne kuma likita ya sanar da ma’auratan cewa ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai ayi mata aiki.

Faston ya tabbatar da cewa, Ubangiji na son ta haifa cikin da kanta ba tare da anyi mata aiki ba. Ya kwatanta yi wa mace aiki a cire da babban haramci. A yayin da matar ta fara nakuda ba tare da anyi mata aiki ba, an rasata da jinjirin. Dukkansu basu fito da rai ba, sun rasa rayukansu wajen kokarin haihuwa ta yadda fasto yace ba tare da bin umarnin likita ba.

Yaw Asamoah Akowuah, mawallafin labarin ya bayyana cewa yi wa mace aiki ba haramun bane, don haka mutane su gane. Ga abinda ya rubuta: “A makon da ya gabata, na bayyana yadda wasu fastoci suka mayar da yiwa mace aiki a cire da babban zunubi.

DUBA WANNAN: Wata jihar ta zabge ma'aikatunta zuwa 16

Wani abokina ya rasa matarsa a makon da ya gabata saboda a coci an ce masa babban zunubi ne ya bari a yiwa matarsa aiki. A duba lafiyarta ta karshe da aka yi a asibiti, an gano cewa ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai likita yayi mata aiki.

“Bayan abokina ya sanar da fasto, sai ya sanar dashi cewa ya yi imani da Ubangiji don bai amince ayiwa matar aiki ba. Zata iya haihuwa da kanta.”

A lokacin da naji wannan zancen, sai na tambayi kaina, yaushe aiki ya zama haramun? Me yasa ake amfani da sunan ubangiji ake saka tsoro a zuciyar mata masu juna biyu?

A takaice dai haka matar ta gwada nakuda don haihuwar jinjirin, amma bata fito ba, hakazalika jinjirin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel