Tirkashi: Likita ya haramtawa mata mai shekaru 36 haihuwa, bayan ta haifi 'ya'ya 44 a duniya

Tirkashi: Likita ya haramtawa mata mai shekaru 36 haihuwa, bayan ta haifi 'ya'ya 44 a duniya

- Likitoci a kasar Uganda sun haramtawa wata mata mai shekaru 36 haihuwa bayan da ta haifa yara 44

- Mariam ta haifa tagwaye shida, 'yan uku sau hudu da kuma 'yan hudu sau biyar

- A cikin haihuwa 15 ne ta samu yara 44 amma ta taba rasa 6 a wajen haihuwa, 38 na nan a raye

Likitoci a kasar Uganda sun haramtawa wata mata mai shekaru 36, mai suna Mariam Nabatanzi haihuwa. Sunyi hakan ne bayan da ta haifa yara 44 wadanda suka hada da tagwaye, jeri-jeri.

Mariam ta yi aure ne a shekaru 12 kuma ta auri wani mutum ne mai shekaru 40. Shekara na zagayowa kuwa ta fara zazzago yara.

Likitoci sun gano cewa tana da manyan kwayoyin halitta kuma jikinta na samar da kwaiyaye masu yawa a wata, don haka take iya samun cikin fiye da yaro daya a lokaci daya.

KU KARANTA: Allah mai iko: Likitoci sun samu nasarar raba wasu yara da aka haifesu a hade, bayan shafe awa 13 suna tiyata

Ta haifa tagwaye shida, 'yan uku har sau hudu sai kuma 'yan hudu sau biyar. Tayi ciki sau 15 a rayuwarta kuma ta haifa yara 44 a duniya. Ta taba rasa yara shida a lokacin haihuwa amma ta iya rainon 38. A don haka ne likitoci suka rasa zabin da ya wuce hana Mariam kara haihuwa.

Ita kanta ta san tsayar da haihuwar shine yafi, shiyasa Mariam take ta farin ciki. Mariam ta bayyana yadda ta taba bukatar likitoci da su tsayar mata da haihuwa a lokacin da ta haifa tagwaye kadan. Amma sai suka ce mata hakan zai iya jawo mata wasu illoli na daban a lokacin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel