Kana taka Allah na tashi: Matar aure da ta shafe shekara bakwai tana neman haihuwa ta mutu awanni kadan bayan ta haifi 'yan hudu

Kana taka Allah na tashi: Matar aure da ta shafe shekara bakwai tana neman haihuwa ta mutu awanni kadan bayan ta haifi 'yan hudu

- Wata mata da ta shafe shekara bakwai tana neman haihuwa bata samu ba, Allah ya dauki ranta awanni kadan bayan ta haifi 'yan hudu

- Matar ta haifi jarirai uku mata namiji daya kafin Allah ya karbi rayuwarta

- 'Yar uwarta ce ta wallafa labarin mutuwar ta din a shafinta na Facebook, inda mutane suka yi ta mamaki

Wani gida a Najeriya sun shiga jimami, bayan diyarsu mai suna Adedotun Afusat Feyisara, wacce ta shafe shekara bakwai tana neman haihuwa, ta mutu awanni kadan bayan ta haifi 'yan hudu a ranar Talata 25 ga watan Agustan nan.

Kanwar marigayiyar, Olawale Adedotun Oluwatomisin, ita ce ta wallafa wannan labari a shafinta na Facebook, ta ce marigayiya Afusat ta haifi 'ya'yanta 'yan uku, mata uku namiji daya, a yau Talata, inda kuma yake ranar bikin cikarta shekaru bakwai da aure.

Kana taka Allah na tashi: Matar aure da ta shafe shekara bakwai tana neman haihuwa ta mutu awanni kadan bayan ta haifi 'yan hudu
Kana taka Allah na tashi: Matar aure da ta shafe shekara bakwai tana neman haihuwa ta mutu awanni kadan bayan ta haifi 'yan hudu
Asali: Facebook

"Adedotun Afusat Feyishara, kin zo ki kamar walkiya, kin tafi ba tare da sallama ba. Kin haifi yara mata guda uku da namiji guda daya a ranar da kika cika shekaru bakwai da aure, kin kuma mutu a ranar, mutuwa mai yasa.

KU KARANTA: Abu kamar wasa: Zakuna sun cinye mutumin da ya raine su tun suna yara a lokacin da suke wasa da shi

"Kalmomi baza su iya bayyana yadda kika zama ta daban ba. Koda yaushe kina sauraron mutum, kece abokiyar hira ta. Kece bango abin dafawa a lokacin damuwa. Kece 'yar uwar da babu kamarta, Ban taba tunanin cewa zanyi amfani da hotonki ba bayan kin mutu, amma Ubangiji ya fi mu sanin abinda ke boye. Allah ya dauke ki ya bamu 'yan hudun da kika haifa, zamu dinga tunawa dake har abada. Ina sonki 'yar uwa, kuma zan cigaba da kaunarki har abada," A cewar Oluwatomisin.

Tuni dai an binne Afusat a bisa yadda addinin Musulunci ya tsara.

'Yan uwa da abokanan arziki sun hau shafukan sadarwa suna nuna mamaki akan wannan mutuwa da tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel