Aisha Yesufu: “Munafunci ya hana ayi magana kan satar Dalibai saboda Buhari ne a mulki”

Aisha Yesufu: “Munafunci ya hana ayi magana kan satar Dalibai saboda Buhari ne a mulki”

- Aisha Yesufu ta fito ta yi magana a game da yawan satar dalibai da ake fuskanta

- Yesufu ta ce munafuncin mutane ya hana a rika kuka a kan sace yaran da ake yi

- Wannan Baiwar Allah ta yi kira ga shugabanni suji tsoron Allah, su kare al'umma

Aisha Yesufu ta yi magana a kan sace yara da ake ta yi a makarantun Arewacin Najeriya, ta ce abin sai dai ace "Innalilahi wa inna illaihi rajiun."

A cewar Aisha Yesufu ba a taba ganin ‘yan bindiga su na zuwa su na dauke yara haka ba, amma gwamnati ta yi kunnen shegu, mutane kuma sun yi tsit.

Ta ce: “Wai ba za ayi magana ba saboda Buhari ne shugaban kasa. Amma idan da wani ne, alal misali wani da ba musulmi ba, da tuni an daina munafuncin nan, ana ta fito wa, ana magana.”

“Amma yanzu yawancin mutane an yi tsit, an zauna ana kallon ana dauke yara, Allah kadai ya san abin da aka yi masu” inji Yesufu.

KU KARANTA: Aisha Yesufu ta iyaye shawara su killace 'ya 'yansu

‘Yar gwargwamayar ta ke cewa Ubangiji ne kadai ya san halin da yaran makarantun Arewa su ke ciki na dar-dar. Ta ce: “Wannan abin bai kamata, ba daidai ba ne.”

“Gwamnoni da shugaban kasa su ji tsoron Allah. Talakawan nan su ne su ka zabe su, su ka fito kwansu da kwarkwatarsu, su ka zauna a karkashin rana, su ka jefa maku kuri’a.”

Ta ce: “Mutane su na cikin wani hali, amma masu mulkin da aka zaba sun yi kunnen uwar-shegu."

Duk da an yi sababbin zubin shugabannin hafsun sojoji, jagorar kungiyar BBOG ta ce ba a daina jin labarin ‘yan bindiga sun sace yara a makarantun yankin Arewa ba.

KU KARANTA: Dr. Isa Pantami ya yaba da kokarin Sa’adat Aliyu na kirkiro Helpio App

Aisha Yesufu: “Munafunci ya hana ayi magana kan satar Dalibai saboda Buhari ne a mulki”
Aisha Yesufu Hoto: Legit TV
Asali: UGC

Yesufu ta yi tir da yadda shugaban kasa ya rika yabon tsofaffin hafsoshin sojoji, har ta kai an nada su jakadu a kasashen waje, ta ce don a cigaba da dama wa da su.

Bayan haka Yesufu ta ce ana neman a birne zargin da NSA, Babagana Monguno ya yi na cewa an salwantar da kudin makamai a karkashin tsofaffin hafsun sojoji.

Dazu kun ji cewa mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya tsoma bakinsa a game da satar 'daliban da ake yawan yi a makarantun Arewacin Najeriya.

Gwamna Nyesom Wike ya ce lamarin ya na kuma nema ya zama wani abin darayi a halin yanzu.

Wike ya yi magana ne yayin da ya ke gana wa da karamin Ministan noma da raya karkara, Mustapha Baba Shehuri a lokacin da ya kawo masa ziyara a Fatakwal.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel