Gwamnatin tarayya ta karrama Sa'adat Aliyu da ta kirkiro manhajar da za ta yi maganin fyade

Gwamnatin tarayya ta karrama Sa'adat Aliyu da ta kirkiro manhajar da za ta yi maganin fyade

- Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya jinjinawa aikin Sa’adat Aliyu

- Isa Pantami ya hadu da wannan budurwa da ta kirkiro manhajar hana fyade

- Ministan ya ba shugabar Shamrock Innovation Hub takardar yabo a ofishinsa

Miss Sa'adat Aliyu da ta kirkiro wata manhaja da za ta ba wadanda aka yi wa fyade damar kai kara ba tare da tsangwama ba ta samu lambar yabo.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami FNCS, FBCS, FIIM ya karrama Sa’adat Aliyu a madadin gwammatin tarayya.

Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya mika wa wannan Baiwar Allah takardar yabo saboda kokari na fasahar da ta yi kamar yadda aka sanar a shafin Twitter.

Wannan mutumiyar Kano, Sa'adat Aliyu, ita ce shugabar kamfanin Shamrock Innovation Hub.

KU KARANTA: Wata Baiwar Allah ta ƙera manhajar shigar da ƙorafin fyaɗe

Rahoton ya bayyana cewa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ba Aliyu takarda ta musamman a ofishinsa da ke cikin ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani.

An dauki gajeren lokaci wajen bikin bada wannan wasika ga Miss Aliyu saboda aikin da ta yi.

Ministan tarayyar ya ce wannan budurwa ta yi kokari da ta kawo wannan manhaja a lokacin da ake fuskantar barazanar fyade da lalata da kananan yara.

Wadanda ake yi wa fyade su kan jin kunyar su kai kara saboda tsangwama a al’umma, don haka Ministan ya taya Aliyu murnar wannan fasaha da ta nuna.

KA KARANTA: An ceto wasu mata daga gidan saida jarirai

Gwamnatin tarayya ta karrama Sa'adat Aliyu da ta kirkiro manhajar da za ta yi maganin fyade
Isa Pantami da Sa'adat Aliyu Hoto: @FMoCDENigeria
Asali: Twitter

Pantami ya yi kira ga gwamnati ta taimaka wa mata domin su cin ma burinsu a rayuwa. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan an samu labarin wannan manhaja.

A karshe Ministan ya yi kira ga hukumar NITDA ta hada kai da matasa masu taso wa domin a cigaba da kirkirar na fasaha da za su taimakawa kasar irin wannan.

Kun ji cewa shugabar WTO, Dr. Okonjo-Iweala ta ba Gwamnatin tarayya satar amsar ceto tattalin arziki yayin da ta zauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Dr. Okonjo-Iweala ta ce idan gwamnati ta biyewa samun fetur, za a shiga matsala nan gaba.

Darekta-Janar ta WTO, Ngozi Okonjo-Iweala ta ce ya zama dole gwamnatin tarayya ta fadada hanyar samun arzikin Najeriya, sannan kuma a tsaya tsayin-daka.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel