Da a sace yaranku, gwanda ku killace su a gida, Aisha Yesufu ga iyaye

Da a sace yaranku, gwanda ku killace su a gida, Aisha Yesufu ga iyaye

- Aisha Yesufu ta shawarci iyaye a arewacin Najeriya da su daina tura 'ya'yansu makaranta

- Ta bayyana rashin jin dadinta tare da yin Allah-wadai da yawaitar sace dalibai a yankin

- Hakazalika ta caccaki gwamnatin tarayya da yin rikon sakainar kashi da matsalar tsaro

Aisha Yesufu ta shawarci iyaye da ke tura 'ya'yansu makarantu a jihohin arewacin Najeriya dake fuskantar matsalar tsaro da su hakura su killace yaran na wani lokaci kafin gwamnati ta samar da mafita mai dorewa.

Biyo bayan sace dalibai da aka yi na baya-bayan nan a jihar Kaduna, 'yan Najeriya na ci gaba da nuna juyayi da Allah-wadai da kai hare-haren 'yan bindiga a fadin arewacin Najeriya.

Masu fada aji a kasar, na bayyana ra'ayoyi da shawarwarinsu ga gwamnati hade da iyaye kan matakan da ya kamata a dauka domin magance matsalar da ta dumfaro arewacin Najeriya.

KU KARANTA: 'Yan fashi sun far wa kwastoman banki da nufin kwace kudi N10m

Da a sace yaranku, gwanda ku killace su a gida, Aisha Yesufu ga iyaye
Da a sace yaranku, gwanda ku killace su a gida, Aisha Yesufu ga iyaye Hoto: Premium Times Nigeria
Source: UGC

Aisha Yesufu, wata 'yar gwagwarmaya mai rajin kare hakkin dan Adam ta bayyana ra'ayinta game da halin ha'ula'in da yakunan arewacin ke ciki na matsalar tsaro da yawaitar sace dalibai musamman a jihar Kaduna a makon nan.

A wata hira da wakilinmu na Legit.ng Hausa yayi da Aisha Yesufu, ta bayyana cewa, zai fi zama alheri ga iyaye su killace 'ya'yansu a gida maimakon su tura su a sace su.

"Da a dauke maka yaro gwara yana nan a killace. Yanzu yakamata iyayen yara ace yara su koma gida. Jihohi da yawa sun rufe makarantu.

"A ajiye yara a gida, kuma mu fito kamar yadda muke fitowa muke jefa kuri'a mu cewa gwamnati tayi duk abinda za ta yi ta tabbatar yaranmu zasu kasance karkashin tsaro."

Hakazalika ta caccaki gwamnati kan gazawa wajen kawo mafita mai dorewa game da matsalar tsaro a yankunan na arewacin Najeriya tare da yin halin ko in kula da 'ya'yan talakawa.

"Idan fa mutum talaka ne, wallahi kamar baka da rai, kai ba mutum bane ba a kasar nan. Banda wannan hannun naka da zaka yi amfani wajen dangwala musu zaben basa kallonka da gashi a kai."

KU KARANTA: Dalilan da suka sanya jihar Kano haramta sayar da lemon dan tsami

A wani labarin daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kakkausar kashedi ga ‘yan ta’adda da 'yan bindiga da ke addabar makarantu, yana mai cewa kasar ba za ta bari a lalata tsarin makarantu ba, PM News ta ruwaito.

Shugaban ya yi wannan gargadin ne a cikin wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, a Abuja ranar Asabar.

Buhari ya mayar da martani ne kan mamaye Kwalejin Harkar Noma da Gandun Daji ta Tarayya dake Afaka a jihar Kaduna, da wasu mahara suka yi a ranar Juma’a.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel