Wata 5 da aure, Amaryar attajiri ta bukaci ya saketa bayan maye sunansa da nata a kadararsa

Wata 5 da aure, Amaryar attajiri ta bukaci ya saketa bayan maye sunansa da nata a kadararsa

- An shiga kotu tsakanin Miji da Amaryarsa kan abinda ya siffanta matsayin yaudara

- Watannnisu biyar kacal da aure a kasar Saudiyya

- Amaryar ta ce sai yanzu ta fahimci kuskure tayi wajen auren mutumin da ya tsufa

Wani dattijo dan shekara 70 a kasar Saudiyya ya shigar da amaryarsa kotu watanni biyar bayan aurenta.

A cewarsa, amaryar ta yaudareshi inda ta maye sunansa da nata a takardar mallakin gidansa.

Dattijon ya ce ya aureta watanni biyar da suka shude kuma ta sanya sharadin cewa zai bata waqafin gidansa saboda tsoron kada manyan 'yayansa maza su koreta daga gidan idan ya mutu.

A cewarsa, saboda nacewar da tayi kan haka ya sa ya amince kuma akayi rijistan sunan gidan da sunanta.

Yace ana bata takardun gidan ta shigar da shi kotu inda ta bukaci kawai a raba auren.

DUBA NAN: Gwamna Uzodimma ya sa wa titi sunan shugaba Buhari

Wata 5 da aure, Amaryar attajiri ta bukaci ya saketa bayan maye sunansa da nata a kadararsa
Wata 5 da aure, Amaryar attajiri ta bukaci ya saketa bayan maye sunansa da nata a kadararsa Credit: Life in Saudi Arabia
Source: Facebook

KU KARANTA: Hotunan shugaba Buhari yayin da ya karba bakuncin shugaban kasan Nijar a Aso Rock

Yayinda aka ji dalilin da yasa tayi hakan, ta ce gaskiyar lamari ta aureshi ne don Allah kuma cikin soyayya. Amma daga baya ta gano cewa kuskure tayi saboda ya girmeta da kimanin shekaru 50.

A cewarta, ba ta tunanin za ta ji dadin aure da mutumin da ya bata wadannan shekarun.

Lauyoyi a kasar Saudiyya sun ce karar da dattijon ya shigar kotu ba za tayi wani tasiri ba saboda cikin hayyacinsa ya mayar da gidan nata.

Saboda haka gida ya zama nata.

Labari daga: Urdu News

A wani labarin kuwa, kwana biyar bayan an yi garkuwa da ita, har yanzu ba a san inda wata amarya da za a yi a Kano, Amina Gwani Danzarga take ba.

An tattaro cewa an sace Amina, wacce ke zaune a Unguwar Koki a cikin birnin Kano a ranar Juma'a, kwanaki biyu kafin bikinta.

Ganin karshe da ’yan uwa suka yi wa Amina wacce daliba ce a Kwalejin Tarayya da ke Kano, shi ne yayin da ta fita daga gida zuwa makaranta a yammacin ranar Juma’a.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel