Saboda girmamawa: Gwamna Uzodimma ya sa wa titi sunan shugaba Buhari

Saboda girmamawa: Gwamna Uzodimma ya sa wa titi sunan shugaba Buhari

- Gwamnatin Gwamna Hope Uzodinma ta inganta kayayyakin more rayuwa a jihar Imo

- Shugaba Buhari ya yi magana game da ci gaban jihar Imo

- Hope Uzodinma ya kasance gwamna a shekarar da ta gabata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da hanyoyi biyu a Owerri, babban birnin jihar Imo, wadanda aka kammala cikin shekarar farko na gwamna Hope Uzodinma.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmed, ya bayyana cewa an kaddamar da ayyukan ne ta yanar gizo a ranar Talata, 16 ga Maris.

KU KARANTA KUMA: Abun farin ciki: Dalibar Kano da aka sace ana saura awanni 48 aurenta ta kuɓuta

Saboda girmamawa: Gwamna Uzodimma ya sa wa titi sunan shugaba Buhari
Saboda girmamawa: Gwamna Uzodimma ya sa wa titi sunan shugaba Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ya ce an sauya wa daya daga cikin hanyoyin, mai nisan kilomita 5 a hanyar sakatariyar Tarayya zuwa Bankin Duniya suna zuwa titin Muhammadu Buhari.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugaban a wajen bikin ya yabawa gwamnan jihar Imo, kan sadaukar da kai ga jin dadin mutanen jihar ta hanyar samar da ingantattun kayan more rayuwa.

Buhari ya ce:

”Na yi farin cikin sanin cewa an samu ci gaba sosai wajen kammala su, kuma da dama daga cikin su na cikin wadanda aka kaddamar a matsayin wani bangare na abubuwan girmamawa da aka cimmawa cikin shekara daya.

“Dole ne in yaba wa gwamnatin jihar, a karkashin jagorancin Sanata Hope Uzodinma, kan yadda ta tsara manyan burika a cikin shekara daya kacal a kujerar mulki ta hanyar amfani da wannan lokacin don tantance inda aka kai a tafiyar."

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta sanya ranar bude filin jirgin saman Kano

Ya bukaci gwamnan da ya ci gaba da samun ci gaba tare da hanzarta tafiyar da kyakkyawan shugabanci a jihar.

A wani labarin, a ranar Talata ne aka baiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari lambar yabo mafi girma ta Jamhuriyar Nijar, wanda ake kira da Grand Croix Des Ordre National Du Niger.

Shugaban kasar Nijar mai barin gado, Mahamadou Issoufou ne ya karrama shi da lambar yabon.

Adesina ya nakalto shugaban yana taya Issoufou murnar kammala wa’adinsa na biyu cikin nasara, da kuma lashe babbar lambar yabo ta Mo Ibrahim ta nasarar da ya samu a shugabancin Afrika, yana mai bayyana shi a matsayin shugaban Afirka da ya cancanta.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng