Dokubo Asari ya dawo, ya na yi wa Najeriya barazana, ya kafa sabuwar tafiyar ‘Yan Biyafara

Dokubo Asari ya dawo, ya na yi wa Najeriya barazana, ya kafa sabuwar tafiyar ‘Yan Biyafara

- Mujahid Asari Dokubo ya zama shugaban wata kungiyar ‘yan taware

- Dokubo ne zai jagoranci tafiyar ‘Biafra defacto Customary Government’

- Wannan ne karon farko da tsohon tsageran ya fito a ‘yan shekarun nan

Tsohon tsageran yankin Neja-Delta, Mujahid Asari Dokubo, ya kalubalanci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya na furta gwamnatin Biyafara.

Daily Trust ta rahoto cewa Mujahid Asari Dokubo ya fito ya bayyana kansa a matsayin shugaban wata kungiya ta Biafra defacto Customary Government.

Asari Dokubo ya sanar da haka ne a wani jawabi da wani Uche Mefor ya fitar a matsayinsa na shugaban sashen yada labarai da sadarwa na tafiyar BCG.

Uche Mefor ya ce:

KU KARANTA: Aisha Yesufu da jagoran IPOB Nnamdi Kanu su na cacar baki

“Mu a matsayinmu na mutanen Biyafara, mun tsaida cewa lokaci ya yi da za mu dauki matsayarmu a hannunmu, mu da kanmu da ‘ya ‘yanmu da sauran al’ummomin da za ayi a nan gaba, ‘yanci.”

“Na 'dan dakata kadan, amma na gode wa Ubangiji, lokaci ya yi da za mu yi aikinmu, mu bauta wa kasarmu, na karbi wannan nauyi, zan sadaukar da rayuwa ta 100% a kai.”

Aikina na farko shi ne in bayyana wadanda za su zama ‘yan gaba-gaba a wannnan tafiyar inji Asari Dakubo.

A jawabin ne aka nada George Onyibe da Emeka Emeka Esiri a matsayin sakatare da mai bada shawara kan harkar shari’a na Biafra defacto Customary Government.

KU KARANTA: Mutanen Ibo ba su bukatar kujerar shugaban kasa - Nnamdi Kanu

Dokubo Asari ya dawo, ya na yi wa Najeriya barazana, ya kafa sabuwar tafiyar ‘Yan Biyafara
Asari Dokubo Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Dokubo ya yi kira ga mutanen kasar Biyafara da ke Aba, Abakiliki, Anang, Awka, Calabar, Degema, Eket, Enough, Nsuka, Ogoja, Oji River, Okigwe, Onitsha, Opobo, Orlu, Owerri, Fatakwal, Umuahia, Uyo da Yenegoa su ba wannan kungiya goyon-bayansu.

Mujahid Asari Dokubo ya ce zai kafa gwamnoni da shugabanni da za su rike Birane, sannan ya soki yunkurin da aka yi na hana aiko wa mutanen kudu abinci.

Shugaban kungiyar fafutukar kafa haramtacciyar jamhuriyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu,ya ce Kiristocin Arewa ba su da wata damuwa a kan wargajewar kasar.

Nnamdi Kanu ya bayyana cewa za a ba mabiya addinin kirista da su ke yankin Arewa mafakar siyasa a Biyafara a lokacin da yankin ya bangare daga Najeriya.

Kanu ya jaddada cewa Biyafra ba za ta bari al'ummomin kirista a Arewa su yi aiki da shari'a ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel