Zamu bai wa Kiristocin Arewa mafakar siyasa a Biafra, Nnamdi Kanu

Zamu bai wa Kiristocin Arewa mafakar siyasa a Biafra, Nnamdi Kanu

- Nnamdi Kanu, ya bayyanawa kirirstocin Arewa cewa, suna da gatansu a kasar da yake son kafawa

- Ya nuna damuwarsa da yadda kiristocin Arewa ke karkashin inuwar Shari'ar Islama a Arewa

- Ya tabbatarwa kiristocin cewa, matukar suna son sauya kasa, to Biafra a shirye ta karbe su

Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar fafutukar kafa haramtacciyar jamhuriyar Biafra (IPOB), ya ce Kiristocin Arewa ba su da wata damuwa game da wargajewar Najeriya.

Kanu ya bayyana cewa za a ba wa mabiya addinin kirista na Arewa mafakar siyasa a Biafra lokacin da ta balle daga Najeriya.

Ya jaddada cewa Biafra ba za ta bari al'ummomin kirista a Arewa su lalace da bin Sharia ba.

Shugaban IPOB din ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful ya fitar.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ba zata tirsasa rigakafin Korona a Kogi ba, in ji Mamora

Zamu bai wa Kiristocin Arewa mafakar siyasa a Biafra, Nnamdi Kanu
Zamu bai wa Kiristocin Arewa mafakar siyasa a Biafra, Nnamdi Kanu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sanarwar ta ce: “Mu 'yan asalin Biafra, IPOB, a karkashin jagorancin Mazi Nnamdi Kanu, muna son sanar da al’ummomin Kirista a Arewacin Najeriya cewa ba su da damuwa a batun wargajewar Najeriya.

"Shugaban na mu ya yi wannan alkawarin ne yayin da yake tabbatar musu da cewa za a ba su damar zama kai tsaye a cikin sabuwar kasar Biafra lokacin da Najeriya za ta nemi taimako kamar yadda duk wata kasa da ta fadi ta yi.

“Biafra ba za ta kyale Kiristocin Arewa wadanda a halin yanzu suke cikin inuwar fulani 'yan ta’adda na Islama da za a gasa su da tsarin Shari'a ta Janjaweed Sharia a Arewa da ke da muradin lalata 'yan asalin yankin Arewacin Najeriya ba.

“Shugabanmu ya basu tabbacin rantsuwa da Allah cewa duk wani kirista dan Arewa da ke son zama a kasar Biafra zai iya zuwa ya zauna. Kiristocin Arewa za su samu mafakar siyasa a Najeriya don neman halaliyan aikinsu.”

KU KARANTA: Bayan taron addu'a, Sarkin Kano yace 'yan Najeriya da su amince da rigakafin Korona

A wani labarin, Fitaccen dan gwagwarmayar nan na Yarbawa, Sunday Adeyemo, ya fara tsokano kafa Jamhuriyar Oduduwa, yana barazanar kawar da 'yan siyasar Yarbawa da zasu ki mara wa shirin nasa baya kafin 2023.

A wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu kuma aka fassara, Mista Igboho yayin da yake zantawa da shugabannin Yarbawa da matasa, ya ja kunnen ‘yan siyasan kan rashin nuna damuwar su ga Jamhuriyar Oduduwa.

A cewarsa, bai kamata 'yan siyasar Yarbawa su yi ihun neman shugabanci na 2023 a wannan lokacin ba, sai dai su kasance a sahun gaba na shirin ballewar da shi da sauran 'yan Kudu Maso Yamma ke goyon baya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel