Aisha Yesufu ta yi wa Nnamdi Kanu wankin babban bargo a kan Fulani makiyaya

Aisha Yesufu ta yi wa Nnamdi Kanu wankin babban bargo a kan Fulani makiyaya

- Fitacciyar 'yar gwagwarmayar, Aisha Yesufu ta mayar wa Nnamdi Kanu martani bayan ya kira ta da mai surutu kuma mahaukaciya

- Dama Nnamdi Kanu ya wallafa wani bidiyo wanda jami'an tsaron kudu suka auka wa makiyaya a jihar Abia suka kore su kuma suka kashe musu shanu

- Bayan ganin wannan wallafar ne Yesufu ta caccaki wannan al'amari, bayan caccakar ne ya kira ta da mahaukaciya ita kuma ta kira shi da Shekau amma na bogi

Fitacciyar 'yar gwagwarmayar nan, Aisha Yesufu sun yi cacar baki da Nnamdi Kanu a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A ranar Lahadi, 31 ga watan Janairu Nnamdi Kanu ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook inda yake nuna jami'an tsaron kudu, ESN, suna hantarar Fulani a sansaninsu dake Isuikwuato, jihar Abia, inda suka yi ta fatattakarsu suna kashe musu shanu.

Wannan bidiyon ya fusata Yesufu, inda ta caccaki lamarin har take cewa hakan bai dace ba.

Kamar yadda ta wallafa a Twitter: "Wannan sam bai dace ba. Bai kamata a ce muna daukar doka a hannayenmu, muna kisa da lalata dukiyoyi. Dole ne mu san yadda za mu dinga hakuri da junamu idan ran mu ya baci. Ya kamata mu dinga bin doka."

Aisha Yesufu ta yi wa Nnamdi Kanu wankin babban bargo a kan Fulani makiyaya
Aisha Yesufu ta yi wa Nnamdi Kanu wankin babban bargo a kan Fulani makiyaya. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Facebook

Kanu, a wata takarda da ya wallafa a ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu ta sakataren shi na yada labarai, Emma Powerful, inda ya mayar da martani yace: "Idan kina daya daga cikin dabbobin da suke ma'adanar dabbobi masu fama da cuta, ina fatan cutar ta kashe ki. Mu a gabas ba dabbobi bane, kuma ba za mu taba zama mu lankwashe kafa ana yi mana yadda aka ga dama ba. Ba za mu taba zama bayi ba. Ku tambayi turawa.

"Ba za mu bar Fulani suna kashe-kashe a yankinmu ba. Za ku iya cigaba da hakuri da azabar da suke yi muku, mu kuwa bamu ga zamu iya ba.

"Kuna ina lokacin da ake yanka mutanenmu, ana yi wa wasu fyade, kuma ana garkuwa da wasu a Isuikwuato? Masu surutu da hauka irinsu Aisha Yusufu?"

Aisha ta kara da wallafa a Twitter kamar haka: "Ban ga amsar sa ba! Ya je can ya yi wa wahalallun da suke bin shi, wadanda suka gwammaci maye gurbin kwakwalwarsu da burodi, suna neman gindin zama maimakon taimaka wa rayuwarsu, 'yan wahala."

Bayan ta ga amsar Kanu, ta mayar da martani, inda tace: "Ku fada wa Shekau din ku na bogi bana daya daga cikin mahaukatan da suke ganin darajar gemunsa da karkataccen jikinsa, wanda hakan yake sanya wa suna bin shi kamar karnuka."

Ta kara wata wallafa wacce ta caccaki ESN tana nuna rashin dacewar abubuwan da suke yi da kuma wautar masu goyon bayansu.

KU KARANTA: Hotunan karen wata 6 da za a siyar N1.1m ya janyo cece-kuce a kafar sada zumunta

A wani labari na daban, Anthony Ezonfade Okorodas wani alkali ne a jihar Delta wanda ya bada labarin yadda gwajin DNA ya bankado cewa ba shi ne mahaifin 'ya'yansa uku ba da tsohuwar matarsa.

A wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar 28 ga watan Janairu, Okorodas ya ce ya yanke hukuncin fallasa sirrin ne domin gujewa maganganun jama'a da kuma karya da za a yi a kansa.

Alkalin ya zargi Celia Juliet Ototo, tsohuwar matarsa da barin aurensu na shekaru 11 a lokacin da autansu yake da shekaru shida a duniya, The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel