'Yan kabilar Igbo basu bukatar shugabancin Najeriya - Nnamdi Kanu

'Yan kabilar Igbo basu bukatar shugabancin Najeriya - Nnamdi Kanu

- Shugaban masu tada kayar baya don rajin kafa jamhuriyar Biafra, Mazi Nnamdi Kanu ya ce kabilar Igbo bata bukatar shugabancin kasar nan

- Kamar yadda ya bayyana yayin zantawar shi da gidan rediyon Biafra, ya ce a lokacin rayuwar shi ne za a kafa jamhuriyar Biafra don haka basu bukatar shugabancin kasar Najeriya

- Nnamdi Kanu yayi tsokaci a kan kafa sabon salon tsaro na Amotekun, amma yace akwai bukatar gwamnonin su nemi hadin guiwar Biafra

Shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu ya ce ba zai yuwu dan kabilar Igbo yayi mulkin kasar ba.

A yayin zantawa da gidan rediyon Biafra, Kanu ya ce hakan ba zai yuwu bane saboda a lokacin rayuwar shi ne za a samu kafa jamhuriyar Biafra.

Ya kara da bayyana cewa, jama'ar yankin Kudu maso gabas basu bukatar hayewa kujerar shugabancin Najeriya.

Kanu ya kara da yin tsokaci a kan yadda gwamnonin Kudu maso gabas suka kafa sabon yanayin tsaro na Amotekun. Ya ce don kafawa ko inganta sabon salon tsaron, akwai bukatar hadin guiwar IPOB kamar yadda jaridar Information.ng ta ruwaito.

'Yan kabilar Igbo basu bukatar shugabancin Najeriya - Nnamdi Kanu
'Yan kabilar Igbo basu bukatar shugabancin Najeriya - Nnamdi Kanu
Asali: UGC

KU KARANTA: Sha'awar juna ce ta kama mu muka yi lalata - Wanda yayi garkuwa da matar aure

A wani labari na daban, wani mai garkuwa da mutane mai shekaru 27 mai suna Saidu Iliya da ke kauyen Gada Yeregi a karamar hukumar Lavun ta jihar Neja, ya bayyana yadda yayi lalata da wata mata mai matsakaicin shekaru.

Iliya yayi garkuwa da matar ne kuma sai yayi lalata da ita yayin da yake jiran mijinta ya biya kudin fansa.

Sa'ar shi ta kare ne a yayin da wata rundunar hadin guiwa ta 'yan sanda da 'yan sintirin da ke kauyen Vunu suka kama shi.

A lokacin da aka tambayeshi ko ya yi amfani da kwaroron roba wajen lalatar da yayi da ita, sai yace, "banyi amfani dashi ba don da yardar juna muka yi ba fyade nayi mata ba."

An gano cewa, a ranar 5 ga watan Maris ne wani Mohammed Sani da ke sansanin Fulani na Vunu da ke Luvun ya kai rahoton cewa wasu mutane dauke da makamai sun kai hari gidan shi inda suka sace matar shi.

Jaridar Northern City News ta gano cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci naira miliyan 10 na kudin fansa amma daga baya sai suka sasanta a naira dubu dari shida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng