Ministan Sadarwa Isa Pantami Ya Ba Kamfanonin Sadarwa Umarnin Dakatar Da Shirinsu Akan USSD

Ministan Sadarwa Isa Pantami Ya Ba Kamfanonin Sadarwa Umarnin Dakatar Da Shirinsu Akan USSD

- Ministan sadarwa Isa Pantami ya bama kamfanonin sadarwa umarnin su dakatar da shirin da sukeyi na rufe amfani da USSD

- Ministan ya bayyana haka ne a wani saƙo daya fitar ranar Asabar ta hannun mai taimaka masa, Femi Adeluyi.

- Ya kuma gayyaci duk masu ruwa da tsaki da suka haɗa da; CBN, kammfanonin sadarwa domin a tattauna kan Lamarin

Ministan sadarwa, Isa Pantami ya umarci dukkanin kamfanonin sadarwa na ƙasar nan da su dakatar da shirin da sukeyi na rufe amfani da USSD na wasu bankunan ƙasar nan.

Umarnin ministan na cikin wani saƙo da ya fitar ranar Asabar ta hannun mataimakinsa, Femi Adeluyi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Shida Duk 'Yan Gida Ɗaya a Jihar Osun

Kamfanonin sadarwar dai sun sanar da zasu rufe amfani da USSD ɗin ne saboda bashin 42 biliyan da suke bin bankunan da abun zai shafa, kuma shirin nasu zai fara aiki ne daga ranar Litinin 15 ga watan maris.

A saƙon da mai taimakawa ministan ya fitar yace:

"Ministan sadarwa Isa Pantami ya umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su dakatar da shirin su n hana amfani da lambobin USSD wajen mu'amala da bankuna a Ƙasar nan."

Ministan Sadarwa Isa Pantami Ya Ba Kamfanonin Sadarwa Umarnin Dakatar Da Shirinsu Akan USSD
Ministan Sadarwa Isa Pantami Ya Ba Kamfanonin Sadarwa Umarnin Dakatar Da Shirinsu Akan USSD Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da wasu gidaje a jihar Borno

"Kamfanonin sadarwan sun yanke wannan hukunci ne na rufe amfani da USSD ɗin saboda bashin kuɗaɗen da suke bin bankunann kasuwanci waɗanda ke amfani da USSD ɗin wajen mu'amala da kwastomomin su." a cewarsa

Pantami ya bayyana cewa ya rubuta wasiƙa zuwa gwamanan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, a kan ya bawa bankuna umarnin su biya wannan bashin da ake binsu.

"Domin samar da maslaha akan wannan lamarin, Pantami ya kira taron masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da; Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Shugaban hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC), da kuma kamfanonin sadarwa." saƙon ya bayyana.

An shirya yin wannan taron ne a ranar Litinin 15 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

A wani Labarin kuma Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Litinin 1 ga watan Sha'aban

Hakan ya biyo bayan rashin ganin jinjirin wata, yayin da watan baya ya ciki kwanaki 30 cif.

Watan Sha'aban dai shine watan da yake na karshe, daga shi sai watan azumin Ramadan na shekara-shekara.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel