Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da wasu gidaje a jihar Borno

Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da wasu gidaje a jihar Borno

- Wasu gidaje da ba a san adadinsu sun kone kurmus sakamakon wata wuta da ta tashi tsakar dare

- An ruwaito faruwar wannar gobara a jihar Borno, yayin da wutar ta ci ta cinye wasu kauyuka

- Ba dai ba da rahoton rasa rai ba, amma alamu sun nuna an yi asarar dukiyoyi masu yawa

Gidaje da yawa sun yi kaca-kaca a wata gobara da ta tashi a garin Gajiganna da ke karamar hukumar Magumeri a jihar Borno.

Wutar da ta fara daga karfe 2 na dare, an ce iska mai karfi ce ta tunzuro ta zuwa gidajen.

Wani dan asalin Gajiganna, Baa Kaka Ibrahim, wanda ya yi magana ta wayar tarho, ya ce wutar “ta tashi ne daga rufin wani gida jim kadan da isowar wani mutum can.

"Kuma saboda gidajen da ke makwabtaka da su an yi su ne daga karare da ciyawa haɗe da iska mai ƙarfi, gobarar ta bazu zuwa wasu sassan garin cikin sauri bayan da ta fi karfin mazaunan da ke amfani da ruwa da yashi don kashe ta.”

KU KARANTA: Wasu jami'o'in Kotono 8 da dalibansu ba a amince su yi bautar kasa ba (NYSC)

Ya ce an kona gidaje da dama da kantuna da kayayyaki masu tsada a cikin garin da ke yankin arewacin jihar, wadanda aka ce rikicin ya fi shafa.

Yankunan da gobarar ta shafa sune Gamboiri, Kangiri, Umara Misulali, Baare, Granbori, Tunjiram da Swindi.

Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da wasu gidaje a jihar Borno
Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da wasu gidaje a jihar Borno Hoto: Premium Times
Source: Twitter

Irin wannan tashin gobara ya faru a wani matsuguni na wucin gadi na mutanen da tashin hankali ya raba da gidajensu a Maiduguri, babban birnin jihar, a watan da ya gabata.

Daily Trust ta tattaro cewa a lokacin da aka shawo kan wutar awanni kadan, kusan rabin garin ya barnata.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Litinin 1 ga watan Sha'aban

A wani labarin, Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce ta kashe wata gobara da ta kone ofisoshi guda 11 kurmus a sansanin sojoji na Bukavo da ke jihar.

Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Juma'a, a cewar rahoton kamfanin labarai na NAN.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel