Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Shida Duk 'Yan Gida Ɗaya a Jihar Osun

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Shida Duk 'Yan Gida Ɗaya a Jihar Osun

- Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kashe mutum shida duk yan gida ɗaya a jihar Osun

- 'Yan bindigan sun farma garin Wasinmi, dake kan hanyar Ife/Ibadan da tsakiyar dare inda suka fara harbi kan me uwa da wabi

- Hukumar 'yan sandan jihar ta bakin me magana da yawunta ta tabbatar da faruwar lamarin, kuma ta tabbatar da kisan mutum shida 'yan gida ɗaya

Wasu 'yan bindiga daɗi da ba'a san ko suwaye ba sun kashe mutane shida 'yan gida ɗaya a wani gari mai suna Wasinmi, jihar Osun.

Garin da abun yafaru nakan babbar hanyar Ife/Ibadan.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun farma ƙauyen ne da tsakiyar dare suka fara harbin kan me uwa wabi.

KARANTA ANAN: Shehu Sani ya bayyana yadda 'yan bindiga suka kara zama abin tsoro a Kaduna

Wakilin Premium Times ya gano cewa jami'an OPC da na 'yan sa kai sun shiga dajin yankin don gano waɗannan suka kai wannan mummunan farmakin.

Hukumar 'yan sandan jihar Osun ta bakin mai magana da yawunta, Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Shida Duk 'Yan Gida Ɗaya a Jihar Osun
Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Shida Duk 'Yan Gida Ɗaya a Jihar Osun Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Wasu jami'o'in Kotono 8 da dalibansu ba a amince su yi bautar kasa ba (NYSC)

Yemisi Opalola, ta bayyana ma manema labarai cewa:

"Kisan ya faru ne a wani yanki da ake kira Wasinmi, kuma dukkan waɗanda aka kashe 'yan gida ɗaya ne. Kwamishin 'yan sandan jihar Ogun na garin da abun yafaru a yanzun haka da muke wannan maganar daku."

"Mun kuma ɗauki matakin gaggawa wajen tura jami'an 'yan sanda garin da abun yafaru," a cewarta.

Rahotanni na nuna cewa a sati biyun da suka gabata lamarin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a jihar ta Ogun, Satar mutane da kashe-kashe na ƙara yawaita duk da kokarin da jami'a tsaron 'Amotekun Security Operatives' na ganin sun kawo ƙarshen lamarin.

A wani labarin kuma An garƙame makarantar da aka sace ɗalibai a Kaduna har sai baba ta gani

An kulle makarantar FCFM dake afaka, Jihar kaduna har sai baba-ta-gani bayan sace ɗaliban makarantar 39 a daren Alhamis ɗin data gabata

A halin yanzu, ɗaliban dake hannun 'yan bindigar sunyi kira da akawo musu ɗauki a wani faifan bidiyo da aka saki jiya.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwanan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano. Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: