Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Litinin 1 ga watan Sha'aban

Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Litinin 1 ga watan Sha'aban

- Sarkin musulmi na Sokoto ya ayyana ranar Litinin15 ga Maris a matsayin 1 ga watan Sha'aban

- Hakan ya biyo bayan rashin ganin jinjirin wata, yayin da watan baya ya ciki kwanaki 30 cif

- Watan Sha'aban dai shine watan da yake na karshe, daga shi sai watan azumin Ramadan na shekara-shekara

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Litinin 15 ga Maris, a matsayin ranar farko ta watan Sha’aban 1442AH, The Guardian ta ruwaito.

Abubakar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini, majalisar masarautar ta Sokoto ya fitar.

KU KARANTA: Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18

Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Litinin 1 ga watan Sha'aban
Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Litinin 1 ga watan Sha'aban Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

“Kwamitin Shawara na Majalisar Masarautar Muslunci kan harkokin Addini tare da hadin gwiwar kwamitin kula da watanni na kasa ba su samu wani rahoto da ke tabbatar da ganin jinjirin watan ba.

“Wannan na sabon watan Sha’aban din 1442AH kenan, a ranar Asabar 13 ga Maris, wanda yayi daidai da ranar 29 ga Rajab 1442AH.

“Saboda haka, Lahadi 14 ga Maris, za ta zama 30 ga Rajab 1442AH.

Sanarwar ta ce: "Sarkin Musulmi ya karbi rahoton, kuma bisa haka ya ayyana ranar Litinin 15 ga Maris, a matsayin ranar 1 ga watan Sha'aban 1442AH."

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Sha’aban shi ne wata na takwas a kalandar Musulunci, wanda ke zuwa kafin fara azumin watan Ramadan.

Sha’aban shine watan karshe kafin watan Ramadan da Musulmai suke amfani dashi don tantance ranar farko ta azumi.

KU KARANTA: Mijin Zahra Buhari ya nuna hotunansa tare da zakin da yake wasa dashi a gida, ya jawo cece-kuce

A wani labarin, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su amince da allurar ta Oxford-AstraZeneca ta Korona.

Ya yi kiran ne a fadarsa jim kadan bayan wani taron addu’a na musamman da aka gudanar domin tunawa da cikarsa shekara daya a kan karagar mulki.

Alhaji Aminu Bayero wanda ya hau karagaa ranar 10 ga Maris, 2020, kwana guda bayan da Gwamnatin Jihar ta tsige tsohon sarki Muhammadu Sanusi II, ya ce masarautar ta samu damar gyara alakarta da gwamnati a cikin shekara guda da ta gabata.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.