An yi an gama: Dalilin Gwamnatin Buhari na dakatar da ba Matasa tallafin kudi - Ministan wasanni
- Ma’aikatar wasanni ta ce ba za a sake rabawa Matasa tallafin ruwan kudi ba
- Sunday Dare ya ce Gwamnati za ta koma bada aron kudi ne a madadin tallafi
- Gwamnatin Najeriya ta rabawa Matasa 460, 000 tallafin COVID-19 N500, 000
Gwamnatin tarayya ta daina bada ruwan kudi a matsayin tallafi ga matasa, ta ce za ta koma ba matasan aron kudi ne a Najeriya.
Jaridar Punch ta rahoto Ministan matasa da cigaban wasanni na kasa, Sunday Dare ya na wannan bayani a garin Awka, jihar Anambra.
Ministan ya yi jawabi ne a karshen taron kwanaki biyu na kara wa juna sani da hukumar aikin gona ta IITA, Ibadan ta shirya a Awka.
IITA ta gudanar da taron ne tare da cibiyar binciken aikin gona ta Umudike da cibiyar International Fund for Agricultural Development.
KU KARANTA: Ba a fahimci maganar da na yi kan ‘baton-dabon’ kudin makamai ba – NSA
A cewar Ministan, ba a raba kason tallafin da ake ware wa domin matasa, a wasu wuraren ma ya yi ikirarin ana facaka ne da kudin.
“Ganin haka, mu ka yanke ba za a sake bada tallafi ga matasa ba, a maimakon haka za a rika ba su bashi ne da za su biya bayan wani lokacin da aka yarje, ta yarda wasu dabam za su amfana da irin wannan tsari.” inji Ministan kasar.
Dare ya ce gwamnati ta kirkiro kafafe dabam-dabam da matasa za su amfana ta harkar gona ta hanyar kafa cibiyoyi a Kudu da Arewa.
KU KARANTA: Mai yawon kiwon dabbobi ya koma makaranta, ya zama Malamin Jami’a
Mataimakin darektan bangaren koya wa matasa sana’a da abin yi a ma’aikatar wasanni da matasa, Adamu Usman Kaina, ya wakilci Minista.
Adamu Usman Kaina ya ce matasa 4600 sun amfana da tallafin N500, 000 da gwamnatin tarayyata bada domin rage radadin annobar COVID-19.
Sanatan jihar Imo, Rochas Okorocha ya ce zai sake yin takarar kujerar shugaban Najeriya a 2023, wannan ne zai zama karo na hudu da ya nemi mulki.
Tsohon Gwamnan jihar Imo, ya ce bayan yayi takara har uku babu nasara a 2003, 2007 da kuma 2014, zai nemi sa’ar 2023, kuma ya na sa ran kai labari.
Okorocha ya yarda cewa kasar nan ta shiga wani mawuyacin hali a sakamakon matsalar tsaro.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng