Kudin makamai: Monguno ya gyara zancensa, ya ce tsofaffin hafsoshi ba su yi sata ba

Kudin makamai: Monguno ya gyara zancensa, ya ce tsofaffin hafsoshi ba su yi sata ba

- Babagana Monguno ya ce tsofaffin hafsun sojoji ba su sace kudin makamai ba

- Mai ba Shugaban kasa shawara ya yi maza-maza, ya gyara zancensa da ya yi

- Monguno ya yi karin haske a game da dabon kudin da aka ware na kayan yaki

Ofishin ONSA na mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro ya fito ya yi karin haske a a kan kalaman da ya yi a game da salwantar kudin makamai.

A wani jawabi da ONSA ya fitar, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya ce ‘yan jarida sun rikada kalamansa bayan hirar da ya yi da BBC Hausa.

Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan jawabi da Babagana Monguno ya yi, ya ce a hirar da aka yi da shi, babu inda ya nuna an yi awon-gaba da kudin makamai.

A cewarsa, ya jaddada kokarin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ne na maganin rashin tsaro ta hanyar ba jami’an sojoji duk kayan aikin da suke bukata.

KU KARANTA: Ba a san inda kudi da kayan yakin sojoji su ka shiga ba - NSA

Jawabin da aka fitar a Abuja ya fara da: “Hankalin ONSA ya zo ga wasu rahotanni da gidajen jaridu su ke yi daga wata hira da aka yi da sashen Hausa na BBC.”

“Mu na so mu bayyana cewa an juya abin da NSA ya fada, domin babu inda ya fito bar-baro ya ce kudin makamai sun bace a karkashin tsofaffin hafsoshin tsaro.”

“A hirar, NSA ya shaida wa ‘dan jaridar BBC Hausa, shugaban kasa ya ware makudan kudi da nufin a sayo makamai, amma kayan ba su isa ba, ko ba su karaso ba.”

Jawabin ya ce Janar Babagana Monguno bai nuna wadannan kudi sun bace a lokacin da tsofaffin shugabannin tsaro su ke ofis ba, kamar yadda wasu su ka rahoto.

Kudin makamai: Monguno ya gyara zancensa, ya ce tsofaffin hafsoshi ba su yi sata ba
Janar Babagana Monguno Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Okorocha zai sake yin takarar Shugaban kasa a 2023

“NSA ya kuma sanar da ‘dan jarida Mai girma shugaban kasa ya na bin kadin kwangilar fansar kayan yaki.” Ya ce a kan iya samun canjin lokacin isowar kaya.

Duk masu wasu tambaya a kan sayen makamai sai su tuntubi ma’aikatar tsaro, jawabin ya ce jami’an tsaro na kokarin shawo kan matsalolin da ake fama da su.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hakikance a kan a harbe duk masu yawo da bindigar AK-47. Buhari ya bayyana haka da ya gana da sarakunan gargajiya.

Fadar shugaban kasa ta fito ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada umarninsa na ganin bayan manyan masu laifi, wadanda su ka addabi Bayin Allah.

A taron da aka yi jiya a fadar Aso Villa, Buhari ya ce irin kashe-kashen da ake yi ya na ba shi mamaki.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel