Sanatan APC, Okorocha ya bugi kirji, ya ce shi zai lashe kujerar Shugaban kasa a zaben 2023

Sanatan APC, Okorocha ya bugi kirji, ya ce shi zai lashe kujerar Shugaban kasa a zaben 2023

- Tsohon Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha zai shiga takarar 2023

- Sanata Rochas Okorocha ya ce ya na sa ran zama Shugaban Najeriya

- A baya can, Sanatan ya yi ta neman kujerar Shugaban kasa bai dace ba

Tsohon Gwamnan jihar Imo, Rochas Owelle Okorocha, ya bayyana sa-ransa na cewa zai lashe babban zaben shugaban kasa da za ayi a shekarar 2023.

Sanata Rochas Okorocha mai wakiltar yammacin jihar Imo a majalisar dattawa ya yi wannan bayani ne a jiya, ranar Alhamis, 11 ga watan Maris, 2021.

Jaridar Daily Trust ta ce Rochas Okorocha ya yarda cewa kasar nan ta shiga wani mawuyacin hali a sakamakon matsalar rashin tsaro da ake fama da shi.

Okorocha ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya karbi wata tawagar kungiyar matasa ta 'Anayo Rochas Okorocha' (FOWARO 2023) da ke goyon bayansa.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Rochas Okorocha bai da kunya, Gwamnatin Imo

Jagoran na jam’iyyar APC ya ce a duk neman takarar da yake yi, ya na shan kasa ne tun a wajen zaben fitar da gwani, ya ce a 2023 ne zai samu kai wa ga ci.

Da yake jawabi, Okorocha ya ce: “Na yi takarar kujerar shugaban kasar Najeriya sau uku. Shekaru 20 kenan da na yi takarar farko, a lokacin ina matashi sosai.”

"Na yi takara ne a jam’iyyar ANPP. Daga baya na nemi tikiti a PDP, inda na zo na biyu. Na karshe shi ne na nemi takarar a jam’iyyar APC a 2014.” Inji Sanatan.

“Saboda haka na dade da sanin wannan harka ta takarar shugaban kasa. Wannan karo zai zama na hudu na, kuma ina sa ran zama shugaban kasar Najeriya.”

Sanatan APC, Okorocha ya bugi kirji, ya ce shi zai lashe kujerar Shugaban kasa a zaben 2023
Sanata Rocha Okorocha Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

KU KARANTA: PDP ta yi taro, ta na kitsa dabarun lashe zaben Shugaban kasa

“Ko yaushe na nemi takara, sai in fadi zaben fitar da gwani, wannan karo idan na fito, dole in ci zabe.”

A baya idan za ku iya tuna wa, an ji Rochas Okorocha ya na cewa Najeriya na bukatar ‘Yan siyasan kirki su hada-kai da nufin kawo gyaran da ake hari.

Tsohon gwamnan na Imo, Rochas Okorocha, ya na kiran a samu hadin gambizar ‘yan siyasa na APC da PDP da za su ceto kasar nan daga halin da ta samu kanta.

Sanatan yace akwai 'yan siyasa na banza a cikin jam’iyyun PDP har da ma APC da yake ciki.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel