Labarin wani jajirtaccen Agwai Mai gadi da ya zama 'Lakcara' a babbar Jami’ar Tarayya
- A 2012 aka dauki Adamu Garba aikin gadi a Jami’ar Tarayya da ke Wukari
- Adamu Garba ya hada aiki da karatun digiri a wannan jami’a ta jihar Taraba
- Yanzu Allah ya yi, wannan Agwai ya yi Digiri, an dauke shi Malamin jami’a
Mun samu labarin wani Bawan Allah mai suna Adamu Garba, wanda ya fara daga kiwon dabbobi, har ya yi karatu, yanzu rayuwarsa ta canza har abada.
Life in Arewa ce ta kawo labarin wannan Bafullatani, Adamu Garba, wanda a baya kowa ya san shi da kiwon dabbobi, sai daga baya ya samu aikin gadi.
An dauki Malam Adamu Garba gadi ne a babban jami’ar tarayya ta Wukari, jihar Taraba.
Idan za a tuna, an bude wannan jami’a ne tare da wasu jami’o’in gwamnatin tarayya a fadin kasar nan a lokacin da Goodluck Jonathan yake kan mulki.
KU KARANTA: ‘Dan Majalisar Tarayya ya kai Gwamnan Taraba kara a kotu
A ranar 1 ga watan Satumban 2012, aka dauki wannan Bafullace aikin gadi a FUWukari, Garba ya samu aiki da matakin albashi na mai karamin karatu.
Daga wannan lokaci ne wannan mutumi ya rabu da kiwon dabbobi, ya zama mai gadi a jami’ar.
Ana cikin tafiya a haka kuma sai Adamu Garba ya koma aji, ya fara karatun Digiri a wannan jami’a dai ta Wukari, kuma Ubangiji ya ba shi babbar nasara.
Garba ya yi digirinsa a bangaren karantar halayyar mutane watau Sociology a makarantar da yake gadi. Ba kasafai mutane su ke samun wannan damar ba.
KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun dura Kauye da ido-na-ganin-ido, sun kashe mutane
Wannan mutumi wanda agwai ne, ya kammala digirinsa na farko da matakin 2’1, abin da ake kira Second Class Upper, wannan shi ne matsayi na biyu a jami’a.
Dama can Garba ya yi NCE don haka aka dauke shi zuwa aji na biyu. A wannan shekarar ya kammala karatu, aka dauke shi aikin karamin malamin jami’a.
Dazu mun kawo maku rahoton wani bincike da aka yi a kan abin da ya sa tsofaffi masu iyali da Naira a hannunsu su ke karbewa samarin zamanin yau 'yan Mata.
‘Yan mata su na kyale sa’o’insu, sun koma neman tsofaffi masu garin kudi a aljihu. Wannan lamari na 'wuf' ya bar samari masu taso wa su na yawon koka wa.
Wasu sun ce daga cikin dalilan shi ne manyan maza sun fi dukiya da iya tarairayar 'diya mace.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng