Yadda Ironsi, Gowon, Obasanjo suka dasa tubalin rashin tsaro a Najeriya, Sarkin Musulmi

Yadda Ironsi, Gowon, Obasanjo suka dasa tubalin rashin tsaro a Najeriya, Sarkin Musulmi

- Sarki Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III ya ce Ironsi, Gowon da Obasanjo ne suka kafa tushen rashin tsaro a kasar nan

- Shugaban majalisar sarakunan ta Najeriya ya ce dokar dokar Ironsi ta 1966, Gowon ta 1967 da Obasanjo 1976 ne suka kwacewa sarakuna iko

- Ya tabbatar da cewa Turawan mulkin mallaka suna da hikima a dokokin da suka tsara da kuma ikon da suka baiwa sarakunan gargajiya

Shugaban majalisar sarakunan kasar nan kuma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, a ranar Alahmis yace mulkin janar Aguiyi Ironsi, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo ne suka bar masarautun gargajiya babu kundun tsarin mulkinsu.

A yayin jawabi a wani taro a Abuja ga kwamitin sake duban tsarin mulkin kasar nan na majalisar, ya ce dokar Ironsi ta 1966, Gowon ta 1967 da Obasanjo 1976 ne suka kwace karfin ikon sarakunan gargajiya suka mika ga kananan hukumomi.

Sarkin Musulmin wanda ya samu wakilcin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, ya ce wadannan dokokin ne suka samar da rashin tsaro tare da rashawar da kasar nan ke fuskanta.

KU KARANTA: Ya zama dole mu matsantawa 'yan ta'adda, Buhari ga sarakunan gargajiya

Yadda Ironsi, Gowon, Obasanjo suka dasa tubalin rashin tsaro a Najeriya, Sarkin Musulmi
Yadda Ironsi, Gowon, Obasanjo suka dasa tubalin rashin tsaro a Najeriya, Sarkin Musulmi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce kafin a yi gyaran dokokin kananan hukumomi na 1976, Najeriya tana samun cigaba, zaman lafiya kuma hade da kyawawan al'adun gargajiya.

Yayi kira ga majalisar dattawa da su yi kokarin dawo da wadannan karfin iko na masarautun gargajiya.

Basaraken yace akawai matukar hikima a lamarin Turawa da suka baiwa sarakunan gargajiya tsarin mulki basu bar su kara zube ba.

KU KARANTA: Dole a shafe 'yan bindiga, sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya, El-Rufai

A wani labari na daban, Abubakar Bello, gwamnan Neja yace mulkinsa ba zai taba baiwa tubabbun 'yan bindiga kudi ba, The Cable ta wallafa.

A yayin jawabi a wani taro da yayi da kungiyar 'yan sa kai dake karamar hukumar Mariga, Bello yace wasu wadanda ke ikirarin sun tuba suna karbar kudi ne domin siyan makamai sannan su koma ruwa.

Kamar yadda takardar Mary Noel-Berje, babbar sakatariyar yada labarai ta gwamna Bello, tace duk dan bindigan da ya tuba za a samar masa da abun yi ba tare da an bashi kudi ba a hannunsa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel