Dole a shafe 'yan bindiga, sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya, El-Rufai

Dole a shafe 'yan bindiga, sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya, El-Rufai

- Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yace ya zama dole gwamnati ta gaggauta shafe 'yan bindiga

- Gwamnan ya sanar da cewa lamurransu karara yake nuna kalubalantar karfin ikon mulkin Najeriya

- A cewarsa, abun takaici ne yadda 'yan bindiga ke sace dukiyoyi, su kashe rayuka kuma su hana jama'a zama a gidajensu

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce 'yan bindiga sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya don haka ya zama dole a shafesu.

Ya ce ya zama dole gwamnati a kowanne mataki ta gaggauta ba tare da kasa a guiwa ba wurin kawo karshe al'amuran 'yan bindiga.

El-Rufai yayi wannan tsokacin ne a ranar Laraba yayin gabatar da rahoton tsaro na 2020 na jihar Kaduna, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: Mazauna Kano sun fi son jami'an Hisbah akan 'yan sanda, Shekarau

Dole a shafe 'yan bindiga, sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya, El-Rufai
Dole a shafe 'yan bindiga, sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya, El-Rufai. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Lamurran 'yan bindiga ya matukar nakasa tattalin arziki tare da girgiza zukatan jama'a," yace.

"Lamarin ya kori manoma daga gonakinsu, hakan yasa muka shiga wani hali a bangaren abinci. Jama'a sun rasa gidajensu, an sace dukiyoyi kuma an take hakkin dan Adam na rayuwa lami lafiya.

"Dole ne mu kawo karshen wannan ta'addancin kuma mu baiwa jama'armu damar rayuwa cikin kwanciyar hankali da tsaro. Wannan ne aikin gaggawa da ya dace mu yi."

El-Rufai yace jihar Kaduna ba zata taba tattaunawa ko sasanci ko kuma wani rangwame ga 'yan bindiga ba.

KU KARANTA: Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun yi martanin gaggawa a harin da mayakan ta'addanci suka kai a daren Talata har babban birnin Maiduguri, jihar Borno.

Harin ya zo ne bayan makonni kadan da aka kaiwa Maiduguri mummunan hari inda 'yan ta'addan suka ratsa jami'an tsaron da ke birnin suka wurga bam wanda ya halaka a kalla mutum 15.

HumAngle ta gano cewa mazauna garin a daren Talata sun shiga dimuwa bayan da suka ji karar harbin bindigogi da tashin abubuwa masu fashewa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel