'Yan bindiga da ke ikirarin sun tuba siyan makamai suke da kudaden da ake basu, Gwamnan Neja

'Yan bindiga da ke ikirarin sun tuba siyan makamai suke da kudaden da ake basu, Gwamnan Neja

- Gwamnan jihar Neja yace mulkinsa ba zai taba baiwa tubabbun 'yan bindiga kudi ba

- Ya sanar da cewa komawa suke su siya makamai su cigaba da barna bayan an basu kudi

- Gwamnan ya jinjinawa 'yan sa kai a kan kokarin da suke yi wurin taimakon jami'an tsaro

Abubakar Bello, gwamnan Neja yace mulkinsa ba zai taba baiwa tubabbun 'yan bindiga kudi ba, The Cable ta wallafa.

A yayin jawabi a wani taro da yayi da kungiyar 'yan sa kai dake karamar hukumar Mariga, Bello yace wasu wadanda ke ikirarin sun tuba suna karbar kudi ne domin siyan makamai sannan su koma ruwa.

Kamar yadda takardar Mary Noel-Berje, babbar sakatariyar yada labarai ta gwamna Bello, tace duk dan bindigan da ya tuba za a samar masa da abun yi ba tare da an bashi kudi ba a hannunsa.

KU KARANTA: Bidiyo: Sunday Igboho ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga 'yan sanda, soja da DSS

'Yan bindiga da ke ikirarin sun tuba siyan makamai suke da kudaden da ake basu, Gwamnan Neja
'Yan bindiga da ke ikirarin sun tuba siyan makamai suke da kudaden da ake basu, Gwamnan Neja. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Na zo nan domin mika godiya ga 'yan sa kai tare da karfafa musu guiwa da kuma nuna goyon baya daga gwamnatin jihar ta yadda zasu cigaba da samar da goyon baya ga 'yan sanda da sauran jami'an tsaro wurin yaki da 'yan bindiga," yace.

"Duk wani dan bindiga da ya mika makamansa kuma ya tuba, za a yafe masa kuma a samar masa da abun yi wanda ba za a hada da bashi kudi ba.

"Daga abinda muka gano, tubabbun 'yan bindinga bayan sun karba kudi suna komawa su siya makamai kuma su cigaba da barna."

Gwamnan yace za a samar da makamai ga 'yan sa kan domin inganta yaki da ta'addancin da suka sa gaba.

KU KARANTA: Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa 'yan bindigan Zamfara watanni biyu to mika makamai, Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya sanar da yammacin Talata.

Matawalle yace shugaban kasan ya bada umarnin tura dakaru 6,000 domin murje 'yan bindiga idan suka ki mika makamansu, Daily Trust ta wallafa.

Gwamnan ya sanar da hakan sa'o'i kadan bayan sarakunan gargajiya sun sanar da shugabannin tsaro da suka ziyarci jihar cewa akwai sama da 'yan bindiga 30,000 dake dajikan jihar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: