Ya zama dole mu matsantawa 'yan ta'adda, Buhari ga sarakunan gargajiya

Ya zama dole mu matsantawa 'yan ta'adda, Buhari ga sarakunan gargajiya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga sarakunan gargajiya akan lamurran tsaron kasar nan

- Ya sanar dasu cewa ya zama dole su matsantawa 'yan ta'adda da suka addabi kasar nan da sace jama'a da kashe-kashe

- Buhari yace lamarin arewa maso yamma ya fi bashi mamaki inda jama'ar yankin ne ke sace mutanensu, kashesu tare da kona kadarori

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya jaddada cewa shi ya baiwa shugabannin tsaron kasar nan umarnin su matsantawa 'yan ta'adda, tare da harbe duk wanda suka kama dauke da AK-47 ba bisa ka'ida ba.

Shugaban kasan ya sanar da hakan a taron da yayi da majalisar sarakunan gargajiya a fadarsa dake Abuja wanda manyan sarakunan kasar nan suka samu halarta.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, taron ya samu halartar mai bada shawara kan tsaron kasa, Manjo Janar Babagana Monguno, Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, darakta janar na hukumar jami'an tsaron farin kaya, Yusuf Bichi da darakta janar na NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

KU KARANTA: Namijin da ba zai iya ba budurwa N300K na kasuwanci ba, bai cancanci a aure shi ba, Uche

Ya zama dole mu matsantawa 'yan ta'adda, Buhari ga sarakunan gargajiya
Ya zama dole mu matsantawa 'yan ta'adda, Buhari ga sarakunan gargajiya. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Shugaban kasan wanda yace taron na daga cikin kokarin gwamnati na ganin ta inganta tsaro a kasar nan, yace gwamnatinsa ta samu manyan nasarori a arewa maso gabas da kudu kudu na kasar nan.

Kamar yadda yace, "Amma abinda ke bani mamaki shine abinda ke faruwa a arewa maso yamma inda mutanen da ke da al'ada daya ke kashe juna suna sace shanu tare da kone kadarori.

"A saboda haka, abinda muka tattauna a taron sa'o'i hudu da muka yi wanda ya samu halartar ministocin tsaron cikin gida, tsaro, harkokin waje da shugabannin tsaro, mun bada umarni a bayyane."

"Abinda ya kai ga manema labarai kuma na karanta da kaina shine umarnin harbe wanda aka kama da AK-47.

"Mun rufe iyakokin kasar nan na tsawon shekaru amma rahotannin sirri da na samu sun nuna cewa masu sace mutanen da kashe-kashe basu rasa makamai," yace.

KU KARANTA: Mun biya daruruwan miliyoyi a matsayin kudin fansa ga 'yan bindiga, Sarakuna

A wani labari na daban, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce 'yan bindiga sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya don haka ya zama dole a shafesu.

Ya ce ya zama dole gwamnati a kowanne mataki ta gaggauta ba tare da kasa a guiwa ba wurin kawo karshe al'amuran 'yan bindiga.

El-Rufai yayi wannan tsokacin ne a ranar Laraba yayin gabatar da rahoton tsaro na 2020 na jihar Kaduna, The Cable ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel