Dalibai sun gudu yayinda yan bindiga suka sake kai farmaki jihar Zamfara, sun hallaka 13

Dalibai sun gudu yayinda yan bindiga suka sake kai farmaki jihar Zamfara, sun hallaka 13

- Yan bindiga sun fitittiki daliban makaranta a jihar Zamfara

- A wannan sabon hari, an yi rashin akalla rayuka 13 yayinda aka kwashe shanu

- Hukumar yan sanda ba tayi magana kan wannan lamari ba har yanzu

Wasu dalibai sun tsira da kafarsu a wata makarantar sakandare dake unguwar Damaga, karamar hukumar Maradun dake jihar Zamfara yayinda yan bindiga suka kai sabon farmaki.

Yan bindigan sun dira garin ne ranar Laraba kan babura suna harbin kan mai uwa da wabi.

Akalla mutane 13 suka rasa rayukansu kuma an yi awon gaba da Shanu.

Jaridar Daily Trust ta samu ji daga wani mazaunin garin, Musa Damaga inda ya bayyana abinda da faru.

"Sun dira garin misalin karfe 1 na rana kuma suka fara harbin mutane. Dalibai na daukan darasi a makarantar sakandaren dake garin amma yayinda suka ga yan bindigan, dukkansu suka arce daga aji," cewar Musa Damaga.

"Yanzu da nike muku magana, an gano gawawwakin wadanda aka kashe kuma an kammala shirin jana'izarsu."

Yayinda aka tuntubi kakakin yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce kawai a bashi lokaci.

DUBA NAN: An saki mutanen da ake zargi da haddasa rikicin Shasha, inda aka kashe Hausawa a Ibadan

Dalibai sun gudu yayinda yan bindiga suka sake kai farmaki jihar Zamfara, sun hallaka 13
Dalibai sun gudu yayinda yan bindiga suka sake kai farmaki jihar Zamfara, sun hallaka 13 Hoto: Presidency
Source: Twitter

DUBA NAN: Jerin jihohi 16 da suka samu kasonsu na rigakafin COVID-19 da adadin da suka samu

A bangare guda, gwamnatin jihar Neja ta bada umurnin rufe dukkan makarantun sakandare mallakin gwamnati na tsawon makonni biyu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an yanke wannan shawara ne bayan zaman da akayi tsakanin gwamnatin jihar da jami'an hukumomin tsaro a jihar.

Kwamishanar Ilimin jihar, Hajiya Hannatu Salihu, ta bayyana hakan ranar Alhamis. Ta ce za'a kulle makarantun fari daga ranar Juma'a, 12 ga Maris zuwa 26 ga maris, 2021.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel