Yanzu-yanzu: Gwamnan Neja ya bada umurnin rufe dukkan makarantun sakandaren gwamnatin jihar

Yanzu-yanzu: Gwamnan Neja ya bada umurnin rufe dukkan makarantun sakandaren gwamnatin jihar

- Bayan kulle makarantu 22, gwamnatin Neja ta kulle sauran makarantunta

- Gwamnatin jihar ta bayyana dalilin da ya sa ta dauki wannan mataki

- Jihar Neja ta shiga jerin jihohin da aka kwashe dalibai a makarantun kwana

Gwamnatin jihar Neja ta bada umurnin rufe dukkan makarantun sakandare mallakin gwamnati na tsawon makonni biyu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an yanke wannan shawara ne bayan zaman da akayi tsakanin gwamnatin jihar da jami'an hukumomin tsaro a jihar.

Kwamishanar Ilimin jihar, Hajiya Hannatu Salihu, ta bayyana hakan ranar Alhamis.

Ta ce za'a kulle makarantun fari daga ranar Juma'a, 12 ga Maris zuwa 26 ga maris, 2021.

Duk da cewa a baya an rufe wasu makarantu 22 (11 na kwana, kuma 11 na jeka ka dawo), tace wannan sabon tsari na rufe dukkan makarantun na tsawon makonni biyu zai baiwa jami'an tsaro daman shiri da kuma bincike kan irin hadarin da daliban zasu iya shiga.

A cewarta, idan aka kammala wannan bincike, za'a samu tsarin da zai tabbatar da zaman lafiya da kariya ga daliban, malamai, da makarantun gaba daya.

DUBA NAN: Hotunan daliban Karaga bayan sun kwashe kwanaki 9 hannun yan bindiga

Yanzu-yanzu: Gwamnan Neja ya bada umurnin rufe dukkan makarantun sakandaren gwamnatin jihar
Yanzu-yanzu: Gwamnan Neja ya bada umurnin rufe dukkan makarantun sakandaren gwamnatin jihar
Asali: UGC

KU DUBA: Kasurgurman 'yan bindiga 4 gwamnati ta saki a matsayin fansan daliban Kagara 38

Wannan mataki ya biyo bayan sace daliban makarantar GSC Kagara da tsagerun yan bindiga sukayi.

A ranar 17 ga watan Fabrairu, ‘yan bindiga sun far wa makarantar GSC Kagara kuma suka yi awon gaba da dalibai, ma’aikata, da danginsu.

Bayan kwanaki 9 a daji, yan ta'addan sun sakesu ranar Asabar, 27 ga watan Febrairu, 2021.

Abubakar Bello, gwamnan Neja, ya ce jiharsa ba ta biya fansa ba don sakin dalibai da malamansu da aka sace daga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel