Ganduje: Riga-kafi ne hanyar da ta fi dacewa na kawar da korona

Ganduje: Riga-kafi ne hanyar da ta fi dacewa na kawar da korona

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce yin riga-kafin korona ce hanyar da ta fi dacewa ba kawar da cutar

- Ganduje ya yi wannan jawabin ne ga manema labarai a jihar Kano domin zaburar da Kanawa su rungumi riga-kafin

- Gwamnan ya ce a karon na farko dattawa za a fi mayar da hankali wurin yi wa riga-kafin domin sune suka fi bukatarta

Dr Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya ce riga-kafi ne hanyar da ta fi dacewa na kawar da cutar korona a jihar.

Jihar Kano ta karbi allurar riga-kafin na Covid-19 guda 209,520 a safiyar ranar Laraba.

Da ya ke jawabi yayin taron yan jarida da kungiyoyin masu zaman kansu a ranar Laraba, gwamnan ya bukaci jama'ar jihar su rungumi riga-kafin don dakile yaduwar cutar.

DUBA WANNAN: Bayan haihuwar yara 5, matar manomi ta sake haifar masa ƴan biyar

Ganduje: Riga-kafi ne hanyar da ta fi dacewa na kawar da korona
Ganduje: Riga-kafi ne hanyar da ta fi dacewa na kawar da korona
Asali: UGC

"Wannan wani mataki ne na yaki da annobar Covid-19. Da farko na faɗa muku muna da mataki uku na yaki da annobar, magani, riga-kafi da bada tallafi," in ji shi.

"A wannan matakin, muna wayar da jama'a su rungumi riga-kafin. Mun yi taro da bangarorin jama'a daban-daban kuma har yanzu muna taro kamar yadda muke yi da ku yanzu.

KU KARANTA: Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN

"Akasin riga-kafin Polio, wannan galibi dattawa masu shekaru aka fi yiwa kuma muna fatan ba za mu samu matsala ba domin suna son suyi rayuwa mai tsawo. Ana ganin Kano tana cin nasara a yaki da COVID-19.

"Muna son mu ɗora kan nasarorin mu, hanyar da ta fi dacewa shine ta hanyar riga-kafi don mu kawar da COVID-19, kamar yadda muka yi wa Polio da wasu sauran cututtuka masu kisa."

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel