Bayan haihuwar yara 5, matar manomi ta sake haifar masa ƴan biyar
- Funmilayo Oluwadara, matar manomi a garin Ogbomoso ta haifi yan biyar
- Matar mai shekaru 38 a duniya tana da wasu yaran biyar kafin haifar jariran biyar
- Mai gidanta, Mr Idowu Oluwadara, mai shekaru 40 ya nemi gwamnati da jama'a su tallafa masa
Matar wani manomi, Funmilayo Oluwadara, ta haifi 'yan hudu a karamar hukumar Ogbomoso ta Arewa na jihar Oyo, The Nation ta ruwaito.
Matar mai shekaru 38 ta haifi mata hudu da na miji daya a asibitin Ayoka Clinic and Maternity Center, Oke Ado, Ogbomosho a ranar Alhamis 4 ga watan Maris.
DUBA WANNAN: 'Yar minista da masu garkuwa suka sace da shaƙi iskar ƴanci bayan awanni 48
Mrs Oluwadara, mazauniyar kauyen Ahoroka a garin Oyo, yanzu tana da yara 10 duba da cewa tana da yara biyar kafin ta haifi yan biyar din.
Likitan da ke da asibitin, Dr Afolabi Sikuralahi wanda ya karbi haihuwar yaran yan biyar ya yi wa Allah godiya bisa nasarar da aka samu wurin haihuwar.
KU KARANTA: Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN
A bangarensa, mahaifin jariran biyar, Mr Idowu Oluwadara, mai shekaru 40, manomi dan asalin kasar Togo da ya zo neman aiki a Nigeria ya nemi gwamnati da jama'a su taimaka masu kulawa da jariransa biyar.
A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.
Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.
Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng