Bincike ya fallasa NNPC sun sha kwana da Naira Tiriliyan 4 daga baitul-mali inji Sanatoci

Bincike ya fallasa NNPC sun sha kwana da Naira Tiriliyan 4 daga baitul-mali inji Sanatoci

- Majalisar Dattawa ta ce bincikenta ya nuna NNPC sun karkatar da Naira Tiriliyan 4

- Sanatocin Najeriya sun ce an batar da wannan kudi ne tsakanin shekarar 2010-2015

- A tsawon wannan lokaci, Goodluck Jonathan yake mulki a karkashin jam’iyyar PDP

Kwamitin da ke binciken asusun gwamnati a majalisar dattawa ta jefi kamfanin NNPC da kin dawo da kudin da aka samu daga mai zuwa baitul-mali.

A ranar Litinin, Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kwamitin majalisar dattawan na zargin NNPC da karkatar da Naira tiriliyan hudu a cikin shekaru biyar.

Kwamitin majalisar ya dogara ne da wani bincike na musamman da ofishin babban mai binciken kudi na gwamnatin tarayya ya gudanar a shekarar 2016.

Rahoton babban mai binciken kudi ya ce NNPC sun ki zuba wasu kudin da su ka samu daga shekarar 2010 zuwa 2015 cikin asusun gwamnatin Najeriya.

KU KARANTA: COVID-19: CBN ya sake bude shafin TCF domin bada aron kudi

‘Yan majalisar su na kokarin bin kadin kudin da ma’aikatun gwamnatin tarayya su ke batarwa.

“Daga binciken rahotannin NNPC da aka kai wa kwamitin FAAC a Disamban 2016, mun fahimci akwai Naira tiriliyan hudu da ba a maida cikin asusun FAAC ba.”

Rahoton da majalisar tarayyar ta fitar ya bayyana cewa wadannan kudi sun yi batar dabo a kasar.

Amma NNPC ya maida martani, ya fadi inda aka kai kudin da Sanatocin su ke zargin cewa sun bace, kamfanin ya ce majalisa ba ta yi la’akari da tallafin mai ba.

KU KARANTA: Najeriya za ta karbo bashi daga China domin aikin dogo a Ribas

Bincike ya fallasa NNPC sun sha kwana da Naira Tiriliyan 4 daga baitul-mali inji Sanatoci
Sanatoci a Majalisa Hoto: www.premiumtimesng.com/news
Asali: UGC

Tsakanin 2010 da 2015, NNPC ya ce ya biya Naira tiriliyan hudu a matsayin tallafin man fetur, sannan an kashe biliyan 966 wajen gyaran bututun mai a kasar.

Akwai kuma Naira biliyan 28.6 da aka yi amfani da su wajen cike gibin da ake samu daga tallafin fetur da sauyin farashin kananzir a wannan lokaci da ake magana.

Ku na da labari cewa ana zargin tsohon shugaban kwamitin PRTT, Abdulrasheed Maina ya saci Naira Biliyan 2.1 daga kudin fanshon tsofaffin ma’aikatan Najeriya.

Kotu ta gayyaci Ibrahim Magu, Abubakar Malami SAN, CP Muhammad Wakali (mai ritaya) da kuma Femi Falana SAN su bada shaida a shari’ar Abdulrasheed Maina.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel