Buhari zai kashe fiye da Naira Tiriliyan 1 wajen tada titin jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri

Buhari zai kashe fiye da Naira Tiriliyan 1 wajen tada titin jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri

- Gwamnatin Tarayya za ta gyara titin jirgin kasa na Fatwakal zuwa Maiduguri

- Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin nan a farkon makon nan

- Za a ci bashi daga Sin domin a tada dogon jirgin kasa, aikin ginin tashar jiragen

Jaridar This Day ta ce a makon nan ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin gyara titin jirgin kasa daga Fatwakal zuwa Maiduguri.

Gwamnatin tarayyar za kuma yi aikin babbar tashar ruwan Bonny Deep Sea Port da kuma gina katafaren tashar jirgin kasa a garin Fatakwal, jihar Ribas.

Rahotanni sun bayyana cewa za ayi wannan ayyuka ne ta hanyar neman aro inda bashin zai dauki 85%, yayin da gwamnatin tarayya za ta bada 15% na kudin.

Gwamnatin tarayya za ta karbo aron kudi daga kasar Sin ne domin ayi wadannan ayyuka uku.

KU KARANTA: Ba a samu kudin fara aikin jirgin kasan Ibadan-Kaduna ba – Amaechi

Kamfanin Messrs CCECC Nigeria Limited zai kashe fam Dala biliyan $3.2 kafin ya kammala wannan aiki, a kudinmu na gida, kwangilar za ta ci Naira tiriliyan 1.2.

Da yake jawabi wajen kaddamar da wannan aiki, shugaba Muhammadu Buhari ya ce idan aka gama aikin titin jirgin, za a babbako da kasuwanci a yankin kasar.

“Za a samu kudin aikin ne ta hanyar cin bashi wanda zai dauki dawainiyar 85% na kwangilar, sannan gwamnatin tarayya za ta bada gudumuwar 15%.” Inji Buhari.

“Amfanin wannan aiki ta fuskar tattali da zamantakewan rayuwa da muhalli sun hada da samar da dinbin ayyukan yi a Najeriya, sannan za a ci moriyar fasahar gida.”

Buhari zai kashe fiye da Naira Tiriliyan 1 wajen tada titin jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri
Ministan sufuri, Rotimi Amaechi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Za a kaddamar da aikin titin jirgin kasan Kano-Maradi

Za a inganta kudin shigan Najeriya, kuma aikin ya zo daidai da tsare-tsaren gwamnatin tarayya.”

Dogon na Maiduguri-Fatakwal zai samu tashoshi a Owerri, jihar Imo da Damaturu, jihar Yobe. Jiragen da za a zuba za su iya sharara gudun kilomita 100 cikin sa’a guda.

A shekarar da ta gabata ne aka fara jin gwamnatin Tarayya ta amince ginin titin jirgin kasan.

Kamar yadda Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya fada, gwamnatin tarayya za ta gyara wannan layin dogo, tare da gina wasu sababbin hanyoyi da na daukar lodin kaya.

Tirin irgin kasan zai tashi a kan $3,020,279,549, sai tashar manyan kayan da za a gina za ta tashi a kan $241,154,389.31, sannan tashar cikin ruwan Bonny za ta ci $461,924,369.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel